logo

HAUSA

Yadda Sin ke ba da gudummawa ga ayyukan wanzar da zaman lafiya

2023-12-13 08:49:50 CMG Hausa

Yanzu haka kasar Sin ce kasa ta biyu dake biyan kudaden tallafi da na karo karo ga MDD yadda ya kamata, kuma ita ce kasar da ta fi kowacce ba da adadi mai yawa na dakarun wanzar da zaman lafiya, tun daga shekarar 1990. Wato bayan da kasar ta shiga aikin kiyaye zaman lafiya na MDD, sojoji da ’yan sandanta sun shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya masu tarin yawa. 

Bugu da kari, Sin ta aike da dakarun da yawansu ya kai sama da dubu 70, cikin shekaru 30 da suka gabata. Dakarun wanzar da zaman lafiya na kasar Sin suna gudanar da ayyukan daidaita rikici da kiyaye kwanciyar hankali da kuma ingiza ci gaban tattalin arziki a kasashe da yankuna da dama, kamar Cambodiya, da Kongo (Kinshasa), da Liberiya, da Sudan, da Lebanon, da Sudan ta kudu, da Mali, da Afirka ta tsakiya da sauransu.

A halin yanzu, jami’an wanzar da zaman lafiya na kasar Sin sama da 2500 suna ci gaba da gudanar da ayyuka a wurare daban-daban da kuma hedkwatar MDD. Wannan ya kara shaida kudirin kasar na neman ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma ci gaba sun samu a fadin duniya. 

Saboda irin rawar da suke takawa a sannan duniya, ya sa aka karrama sama da jami’an wanzar da zaman lafiya na kasar Sin 400 dake aiki a Mali karkashin laimar MDD, da lambar yabo ta majalisar, bisa irin gudunmawar da suka bayar ga ayyukan tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Shi ma mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin kiyaye zaman lafiya Jean-Pierre François Renaud Lacroix ya bayyana cewa, yana alfahari sosai da yadda aka gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD har na tsawon shekaru 75, kana ya yabawa kasar Sin kan yadda ta samar da muhimmiyar gudummawa ga sha’anin kiyaye zaman lafiya na MDD.

Jean-Pierre Lacroix ya ce, Sin ta kasance mai goyon bayan MDD wajen gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya, kana ta samar da gudummawa sosai ga ayyukan. Ya kuma bayyana cewa, kasashe da dama sun samu zaman lafiya da kwanciyar hankali sanadiyyar ayyukan kiyaye zaman lafiya, lamarin da ya shaida cewa, ayyukan suna da amfani.

Don haka, yana fatan a nan gaba, MDD da Sin za su kara hadin gwiwa kan ayyukan kiyaye zaman lafiya. Abubuwan da Sin take gudanarwa abu ne da ake ganinsu a zahiri ba maganar fatar baki ba. (Saminu, Ibrahim, Sanusi Chen)