logo

HAUSA

Matt Watterson: Ina jin dadin rayuwa a birnin Jingdezhen

2023-12-12 14:55:10 CRI


Sanin kowa ne kasar Sin kasa ce da ta shahara da tsawon tarihi, a fannin samar da kayayyakin fadi-ka-mutu, tarihin da ya kai sama da shekaru 3000 na sarrafa kayayyakin fadi-ka-mutu.

Sai dai a nan kasar, akwai wani birnin da aka fi sanin shi da nau’o’in kayayyakin fadi-ka-mutu da ya samar, wanda kuma ya samu ci gabansa ne sakamakon kayayyakin fadi-ka-mutu da ya samar. wato birnin Jingdezhen, wanda ke lardin Jiangxi na kudu maso gabashin kasar Sin. A kimanin shekaru sama da 1000 da suka wuce, jiragen ruwa da ke dauke da kyawawan kayayyakin fadi-ka-mutu na kasar Sin sun tashi daga birnin Jingdezhen, kuma suka bi hanyar siliki da ke kan teku har zuwa sassan duniya.

A biyo mu cikin shirin, don jin karin haske.(Lubabatu)