Tian Yu: Basine dake kokarin aiki a kasar Uganda
2023-12-12 15:35:16 CMG Hausa
Bana ake cika shekaru 10, tun bayan da kasar Sin ta bullo da wata muhimmiyar shawara da ake kira BRI, wato shawarar “ziri daya da hanya daya”. Bayan da aka bullo da ita har zuwa yanzu, shawarar tana kawo babban alfanu ga al’ummomin kasashen da suka halarce ta, tare kuma da samar da ci gaba ga dukkanin duniya, da taimakawa ga cimma burin kafa al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. A karkashin shawarar BRI, akwai matasan kamfanonin kasar Sin da dama, wadanda suke aiki tukuru a kasashe daban-daban, inda suke bayar da tasu gudummawa wajen karfafa hadin-gwiwa, da sada zumunta tsakanin kasar Sin da sauran kasashe.
A yankin tafkin Albert na bakin iyakar dake yammacin kasar Uganda, akwai wani filin hako albarkatun man fetur da ake kira Kingfisher, wanda ya zama aiki mafi girma da kasar Sin ta zuba jari a kasar ta Uganda. A ranar 1 ga watan Fabrairun shekara ta 2022, an kaddamar da aikin gina filin hako man fetur na Kingfisher daga dukkan fannoni. Daya daga cikin ma’aikatan kasar Sin a wurin, Tian Yu ya shaida wannan muhimmin lokaci da idanunsa, inda ya ce:
“Muhimman sana’o’in Uganda su ne aikin noma da na kamun kifi. Duk da cewa akwai albarkatun man fetur, amma Uganda din ba ta da kwarewa sosai wajen hakowa da kanta, saboda rashin ingantaccen tsarin masana’antu. Muna fatan ganin aikin gina filin hako man fetur na Kingfisher zai taimaki Uganda wajen dakatar da dogaro kan shigowa da man fetur daga sauran kasashe, kana, zai yi amfani ga kyautata rayuwar al’ummar kasar.”
A farkon shekara ta 2022, Tian Yu, wanda ya shafe shekaru sama da goma yana aiki a kamfanin CNOOC na kasar Sin, ya fara aiki a matsayin manajan kula da hulda da jama’a a kamfanin CNOOC reshen kasar Uganda. A sashin hulda da jama’ar, Tian Yu shi ne Basine daya tilo, inda yake himmatuwa wajen gudanar da ayyuka tare da abokan aiki ‘yan kasar Uganda. Tian Yu ya ce:
“Akwai wata kyakkyawar al’ada a sashin aikinmu, wato a zagayowar ranar haihuwar duk wani ma’aikaci, ko ma’aikaciya, a lokacin muna sayen kek, mu shirya bikin murnar ranar a ofishinmu. A ganina, duk da cewa ba kasaitaccen biki ba ne, amma biki ne mai faranta rai sosai.”
Tian Yu ya ce, yayin fara gina filin, mutanen dake zaune a kewayen yankin tafkin Albert, sun fuskanci kalubale da dama wajen rayuwa, wadanda suka zauna a cikin bukka, kuma ba sa samun wadataccen ruwan sha mai tsafta, har sai sun yi doguwar tafiya tare da tsallake tsaunuka don debo ruwa. Sabili da haka, lokacin da kamfanin CNOOC ke kokarin inganta tsarin hako albarkatun man fetur da iskar gas a Uganda, yana kuma himmatuwa wajen sauke hakkin kyautata rayuwar al’ummar kasar, ciki har da gina muhimman ababen jigilar ruwa, da gina dakunan kwana masu inganci. Kawo yanzu, mazauna wurin na matukar jin dadin rayuwarsu. Tian Yu ya bayyana cewa:
“Mun gina wasu gidajen kwana ga mazauna wurin. Kowane gida na kunshe da dakuna hudu, kuma fadinsa ya kai murabba’in mita 110. Domin kiyaye muhalli, mun kuma saka na’urorin samar da wutar lantarki bisa karfin hasken rana, da na samar da ruwa a kowane gida, ta yadda jama’a za su kara jin dadin rayuwa a ciki. Da muka mika musu makullin gidajensu, sun ce, ba su taba tsammanin za su iya rayuwa a cikin irin wadannan gidaje ba. Akwai tsaro, akwai kuma tsafta, har ma da kebabben kicin da ban daki. Sun ce, a lokacin baya, suna zaune a cikin bukka, wani lokaci idan sun dafa abinci a kofar bukkar, za ta iya kama wuta in akwai iska da ta bugo. Idan hakan ya faru, dole su yi kaura zuwa wani wuri na daban, inda za su tsinci wasu ciyayi don sake gina wata bukka.”
Tian Yu ya kara da cewa, kamfaninsa yana kuma maida hankali kan horas da matasan Uganda, da taimaka musu samun guraban ayyukan yi, inda ya ce:
“Muna samar da horo ga mazauna wajen a fannoni daban-daban. Alal misali, ga masu aikin walda, da masu tuka manyan motoci, wadanda ayyukansu ke shafar bangaren hako albarkatun man fetur da iskar gas, mun ba su horo a wannan fanni. Ga sauran matasan dake zaune a unguwannin kewayenmu, mun kuma samar musu da horon fasahohin ayyuka daban-daban, ciki har da ilimin gyaran motoci, da yin aski, da saka tufafi da sauransu. Har wa yau, mun tuntubi hukumomin gwamnatin wurin, don kaddamar da horo na musamman ga malaman wurare daban-daban na Uganda, da inganta kwarewarsu, da taimakawa ga samar da guraban ayyukan yi masu dorewa.”
Tian ya ce, akwai matasan kasar Uganda da dama, wadanda suka samu kwarewa sosai a fannin hako albarkatun man fetur da iskar gas, ta hanyar halartar horon kasar Sin, inda ya ce:
“Kawo yanzu mun tallafawa wasu daliban jami’’o’in Uganda guda 8, wadanda suka tafi karatu kasar Sin. Lamech Mbangaye na daya daga cikinsu, wanda ya kammala karatu a kasar Sin, har aka karrama shi da lambar yabo da ake kira dalibin da ya yi fice. Da ya koma Uganda, kamfaninmu ya ba shi aikin injiniyan hako rijiyoyin mai. Ya na da sha’awa sosai wajen aiki a kamfaninmu na CNOOC, inda ya samu ci gaba sosai a wadannan shekaru. Labarin Lamech ya yadu har ya jawo hankalin matasan Uganda da yawa, wadanda suka samu karfin gwiwa wajen bayar da tasu gudummawa ga aikin bunkasa sana’ar hako albarkatun man fetur a kasarsu.”
Domin nuna yadda mutanen kasar Sin ke aiki a kasashen waje, gami da muhimmiyar rawar da matasa ke takawa, musamman karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”, Tian Yu, gami da abokan aikinsa sun kuma dauki wasu shirye-shiryen bidiyo, wadanda suka nuna yadda kamfaninsa ke kokarin gudanar da ayyukan hadin-gwiwa tare da kasashe daban-daban, da inganta samun fahimtar juna, da sada zumunta tsakanin matasan Sin da na sauran kasashe.
Yara da matasa, su ne manyan gobe na alakar Sin da Afirka. Tian Yu ya ce, matasan kasar Uganda cike suke da kuzari da karfin-gwiwa, wadanda ke wakiltar makomar ci gaban kasarsu, kuma kafa wani dandali na yin shawarwari da musanyar ra’ayoyi tsakanin matasa, zai taimaka sosai ga raya dangantakar Sin da Uganda, inda ya ce:
“Muna maida hankali kan canzawar zamani da canzawar tunanin matasa, da kokarin gina dandalin musanyar ra’ayoyi tsakanin matasan Sin da Uganda, da bunkasa harkokin bada ilimi ga matasa, da samar da guraban ayyukan yi. A watan Oktobar bara, mun gayyaci wasu jami’an ofishin jakadancin Sin dake Uganda, da malamai da dalibai daga kwalejin Confucius a kasar, gami da kwararrun matasa da ‘yan jaridu, don su ziyarci filin hako albarkatun man fetur da muke aiki. Haka kuma, mun yi shawarwari tare da ma’aikatan Sin da na wurin, da wakilan matasan Uganda, don kara fahimtar abubuwan da suke tunani, musamman wadanda suka jawo hankalinsu, kamar makomar aikin hako albarkatun man fetur da iskar gas da sauransu. Duk wadannan al’amura sun samu babban yabo da amincewa daga manyan shugabannin Uganda, ciki har da shugaban kasar gami da firaministanta.”
Bana ne ake cika shekaru 10 da kasar Sin ta bullo da shawarar “ziri daya da hanya daya”. Matasa sun riga sun zama muhimmin karfi wajen raya al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a sabon zamanin da muke ciki, wadanda ke da nauyin kara yaukaka dankon zumunta tsakanin Sin da Uganda da ma sauran kasashen Afirka. Tian Yu ya ce, zai ci gaba da bada gudummawa don yin kokari tare da matasan Uganda, wajen karfafa hadin-gwiwa, da mu’amala musamman karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”. Tian ya ce:
“Muna fatan kara hadin-gwiwa tare da kamfanonin kasar Sin dake Uganda, da ma sauran kasashen Afirka daban-daban, a wani kokari na kaddamar da ayyukan tallafawa al’ummar wurin, ta yadda nasarorin shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ za su amfani al’ummomin bangarorin biyu. Kana, muna fatan ci gaba da karfafa zumunta tsakanin Sin da Uganda, da ma sauran kasashen Afirka ta hanyar gudanar da ayyukan da suka shafi shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, musamman tsakanin matasa, don su samu damar kara bada gudummawa ga raya shawarar ‘ziri daya da hanya daya’.” (Murtala Zhang)