logo

HAUSA

Syria: Isra’ila ta kai hare-haren sama a wasu wurare dake kusa da babban birnin kasar

2023-12-11 13:36:22 CMG Hausa

Rundunar sojojin Syria ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi wadda ke cewa, sojojin Isra’ila sun kaddamar da hare-hare ta sama, a wasu wurare dake kusa da Damascus, fadar mulkin kasar a daddaren jiya, wadanda suka haddasa lalacewar gine-gine a wuraren.

Sanarwar ta ce, a tsakan daren jiya, da misalin karfe 11 da minti 5 bisa agogon wurin, sojojin Isra’ila sun kaddamar da hare-hare ta sama, a wasu wurare dake kusa da Damascus daga tudun Golan da ta mamaye, to sai dai kuma tsarin tsaron sararin samaniya na Syria ya tare da kuma harbo wasu makamai masu linzami da suka shiga yankin, ko da yake sanarwar ba ta fayyace wuraren da aka kai hare-haren ba. (Safiyah Ma)