logo

HAUSA

ECOWAS za ta sassauta takunkumin da ta kakaba wa Nijar sannu a hankali

2023-12-11 21:22:56 CMG Hausa

 

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) mai mambobin kasashe 15, ta yi alkawarin sassauta takunkumin da ta kakabawa Jamhuriyar Nijar sannu a hankali, biyo bayan sakamakon tattaunawa da gwamnatin mulkin soja ta kasar, bayan hambarar da shugaba Mohammed Bazoum da sojojin suka yi a watan Yuli.

A wata sanarwar da ta fitar a karshen kwarya-kwayar zama na 64 na shugabannin kasashen kungiyar da aka yi a Abuja, babban birnin Najeriya a ranar Lahadi, kungiyar ta kafa wani kwamitin da zai tattauna da gwamnatin mulkin soja a Nijar din, kan bukatar fito da gajeriyar taswirar mika mulki da aiwatar da matakan sanya ido kan hakan. (Ibrahim)