logo

HAUSA

Guterres ya bayyana rashin jin dadi game da kin amincewa da kudurin tsagaita wuta a Gaza

2023-12-11 10:36:21 CMG Hausa

Rahotanni na cewa, sojojin Isra’ila na ci gaba da kutsawa sassan Gaza, inda a jiya Lahadi suka shiga Khan Younis, birni mafi girma a kudancin zirin na Gaza. Birnin dai ya kasance mafaka ga dubban jama’ar da suka tserewa muggan hara-haren da sojojin na Isra’ila ke kaddamarwa.

Wata sanarwa da sojojin Isra’ila suka fitar, ta ce sojojin kasar na kasa, da na sama, da na ruwa, sun kaddamar da hare-hare a wurare sama da 250 dake cikin Gaza. Kaza lika tankokin atilare sun kutsa cikin yankunan zirin masu dandazon jama’a, wanda bai wuce sakwaya kilomita 365 ba, kuma tuni Isra’ila ta rushe akasarin sassan sa. Sanarwar ta ce a karon farko, tun bayan kaddamar da hare-hare ta kasa, sojojin yaki na atilare sun fara daukar matakan soji a cikin zirin Gaza.

Da yake tsokaci game da hakan, babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira da kada a jingine bukatar dakatar da bude wuta bisa dalilan jin kai a Gaza, duk da koma bayan da kudurin tsagaita wutar ya fuskanta a zauren kwamitin tsaron MDD.

Guterres ya ce, "Ina kira ga kwamitin tsaron MDD da ya kara azamar dakile aukuwar mummunan bala’in jin kai, ina kuma sake jaddada kira na da a sake gabatar da bukatar dakatar da bude wuta bisa dalilai na jin kai".

Guterres ya yi wannan tsokaci ne yayin dandalin Doha da ya gudana a kasar Qatar, kwanaki 2 bayan da Amurka ta hau kujerar na ki, don gane da kudurin neman tsagaita wuta a zirin Gaza da aka gabatar a makon jiya, yayin taron gaggawa na kwamitin tsaron MDD.

Hadaddiyar daular Larabawa ce ta gabatar da kudurin, kuma cikin kasa da sa’o’i 24, ya samu amincewar kusan kasashe 100, wanda hakan ke nuni ga yadda sassan kasa da kasa ke da burin ganin an kawo karshen tashin hankali tsakanin Isra’ila da Hamas, domin kare rayukan Falasdinawa a zirin Gaza.

Tuni dai kasashe da dama suka yi tir da matakin Amurka, na kin amincewa da kudurin na neman tsagaita wuta. (Saminu Alhassan)