logo

HAUSA

An fara kada kuri’u a babban zaben Masar

2023-12-11 11:17:56 CMG Hausa

Da misalin karfe 7 na safiyar jiya Lahadi ne Misirawa suka fara kada kuri’un su, a babban zaben kasar na bana, inda ‘yan takara 4 ke fafatawa domin neman lashe kujerar shugabancin kasar, ciki har da shugaba mai ci Abdel-Fattah al-Sisi.

Bisa tsarin zaben, za a rika bude rumfunan zabe sama da 9,000 cikin sa’o’i 12 a kullum, tun daga Lahadi zuwa gobe Talata, inda ake sa ran wadanda suka cancanci kada kuri’a kimanin miliyan 67 za su kammala zabe, bayan kada kuri’un ‘yan kasar mazauna ketare, wanda aka kammala a ranar 3 ga watan nan na Disamba.

A zabukan kasar na shekarun 2014 da 2018, shugaban kasar mai ci Abdel-Fattah al-Sisi ne ya samu rinjaye, da kaso mai yawa na kuri’un da aka kada, a kuma wannan karo ya sake tsayawa takara domin neman tazarce a karo na 3.

Sauran ‘yan takarar da suka shiga zaben na wannan karo, sun hada da dan takarar jami’iyyar SDP Farid Zahran, da na jami’iyyar EAP Abdel Sanad Yamama, da kuma na PRP Hazem Omar.

Hukumar zaben kasar Masar NEA, ta ce alkalan kasar 15,000, da sauran dubban masu sanya ido na gida da na ketare ne ke lura da yadda zaben ke gudana.  (Saminu Alhassan)