logo

HAUSA

Kuri’ar Kin Amincewar Amurka Ta Tsagaita Wuta A Gaza Adawa Ce Ga Bukatar Bil’adama

2023-12-11 17:01:51 CMG Hausa

Kasashen duniya sun nuna bacin rai kan kuria’ar Amurka ta kin amincewa da kudirin tsagaita wuta da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta gabatar, wanda kuma ya samu goyon bayan kasashe fiye da 100, da amincewar kasashe 13 daga cikin kasashe 15 na Kwamitin Sulhu a ranar Juma'a, inda Birtaniya ta kaurace. 

Ta hanyar yin fatali da wannan kuduri, kuria’ar kin amincewar Amurka na nuni da adawarta ga bukatar Bil'adama gaba daya. Wanda ya bayyana munafurcinta a fili game da kimar da take ikirari. Ta ci gaba da ba da kariya ta diflomasiyya game da cin zarafi da ake yiwa al’ummar Gaza, Amurka tana ci gaba da sarrafa dokar kasa da kasa yadda ta ga dama, kuma a wajenta rayuwar wasu mutane ta fi ta wasu mahimmanci, shi ya sa ta daddale hannu kan a ci gaba da kisan gilla a Gaza.  

Ga dai tambaya, ko za a samu adalci ga mutanen Gaza bayan da aka yi fatali da kiran da aka yi na tsagaita wuta? Yayin da gwamnatin Isra'ila, wacce ke da goyon bayan kasashen yammacin duniya, ta ciga da yin kisan-kiyashi a Gaza wanda ya zama abin kunya ga dukkan Bil’adama, shi ke nan Amurka ta zama kasar da ke kawo tsaiko ga samar da adalci a duniya? Ko Amurka take yi a kawar da Falasdinawa daga doron kasa? To lallai yin garambawul ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zama dole, saboda ai duniya ta fi wadannan kasashe biyar mambobin dindindin na kwamitin sulhu girma, kuma dole kudurin duniya ya yi galaba a kan bukatu da manufar wadannan kasashe biyar. 

Sojin Isra'ila sun kashe mutane fiye da 17,400 a Gaza, kashi 70 cikin 100 mata da yara ne tare da raunata fiye da 46,000, a cewar ma'aikatar lafiya ta Falasdinawa, wacce ta ce wasu da dama suna nan makale a karkashin baraguzan gine-gine.   

Kasar Sin a kullun tana kira ga bangarorin da abin ya shafa da su mai da hankali kan manufa guda na kawo karshen rikici a Gaza, ta yadda za a baiwa al’ummar Falasdinu fatar rayuwa da zaman lafiya ta dindindin a yankin Gabas ta Tsakiya. (Muhammed Yahaya)