logo

HAUSA

Sudan ta kudu ta janye sojojinta daga gabashin DRC

2023-12-11 10:05:28 CMG Hausa

Gwamnatin Sudan ta kudu, ta sanar da janye dakarun ta na wanzar da zaman lafiya daga yankin arewacin Kivu na janhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC.

Da yake tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Lahadi, a Juba fadar mulkin kasar, kakakin rundunar sojojin Sudan ta kudu Lul Ruai Koang, ya ce an janye daukacin sojojin kasar da aka tura arewacin Kivu tun a watan Disamban shekarar 2022, a matsayin wani bangare na gamayyar dakarun wanzar da zaman lafiya na hadakar kasashen gabashin Afirka.

Lul Ruai Koang ya kara da cewa, matakin ya biyo bayan sanarwar da gamayyar kasashen yankin suka fitar a ranar 25 ga watan Nuwamba, wadda ta ce janhuriyar dimokaradiyyar Congo ba za ta sabunta yarjejeniyar tsawaita aikin dakarun sojin yankin sama da ranar 8 ga watan Disamban nan ba.

Tun watan Nuwamban 2022, kasashen Kenyan, da Uganda, da Burundi da Sudan ta kudu, suka jibge sojojin su a gabashin janhuriyar dimokaradiyyar Congo, a matsayin wani mataki na dakile fadan da ya barke tsakanin sojojin kasar da ‘yan tawayen M23. (Saminu Alhassan)