logo

HAUSA

Tawagar MINUSMA ta kammala janyewa daga tsakiyar Mali

2023-12-10 15:34:26 CMG Hausa

 

Ofishin watsa labarai na sakatariyar MDD, ya bayyana cewa tawagar dake aikin wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar Mali (MINUSMA) ta kammala janyewa daga yankunan tsakiyar kasar.

A ranar Jumma’a ce dai, tawagar ta rufe sansaninta dake Sevare a yankin Mopti, lamarin da ya kawo karshen kasancewarta a tsakiyar kasar ta Mali.

Rufe sansanin na Sevare, wanda ya biyo bayan rufe sansanonin Ogossagou da Douentza, wani bangare ne na kashi na biyu na janyewar tawagar.

Baya ga cibiyoyi da kungiyoyin farar hula dake Mali, MINUSMA ta taimaka wajen cimma yarjejeniyar zaman lafiya da dama a cikin kasar, tare da ba da tallafin ayyuka da dama a fannonin ilimi, da kiwon lafiya, da samar da abinci, da kuma ruwan sha.

A karshen wannan shekara ne, ake sa ran ragowar jami’an tawagar za su bar kasar Mali, in ban da wadanda ake bukata domin kammala aikin tawagar. (Ibrahim)