Kungiyar kwallon kafa ta kasa MENA A ta samu wani sabon koci
2023-12-10 15:01:09 CMG Hausa
A jamhuriyar Nijar, kungiyar kwallon kafa ta kasa ta bayyana sunan Zaki Badou a matsayin wanda aka baiwa jagorancin kungiyar kwallon kasa ta MENA A, a wannan mako a wani matakin haskaka kwallon kafar Nijar a idon duniya.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
A yayin da kasashen nahiyar Afrika suke haskakawa kan wasan kwallon kafa tare da halartar wasannin kwallon kafa mafi karbuwa ga al’umomin kasashen duniya, musamman ma a kasashen yammacin Afrika, kasar Nijar na ci gaba da neman hanyoyin daidaita harkokin kwallon kafa na kasar a karkashin jagorancin shugabannin wasan tamaula, duk da kokarin kasar wajen halarta wasannin kwallon kafa daban daban a gida da waje, har yanzu haka ba ta cimma ruwa ba, dalilin ke nan da kungiyar kwallon kafa ta kasa cewa da FENIFOOT ke fadi katashin ganin Nijar ta kasance, wata kasar kwallon kafa a nan gaba. Bisa ga wannan tsinkayen ne, kungiyar kwallon kafa ta kasar Nijar, MENA A ta samu wani sabon koci, cewa da Zaki Badou, tsohon dan wasan mai tsaron gida na Marooko bisa wa’adin shekaru 2 da zai fara daga ranar 1 ga watan Disamban shekarar 2023 zuwa ranar 30 ga watan Nuwamban shekarar 2025.
A cewar kungiyar, an dora ma sabon kocin nauyin kai ’yan wasan MENA A wasannin kwallon kafa na cin kofin Afrika CAF ko cin kofin duniya FIFA a tsawon wannan lokaci na kwantaraginsa.
FENIFOOT ta kara jaddada cewa, Zakariyaou Ibrahim ne mataimakin Zaki Badou, da a yanzu haka shi ne kocin rikon kwarya na MENA A.
Tun bayan bayyana sunan sabon kocin MENA A Nijar, ’yan kasa suka nuna fatansu na ganin Nijar ta dawo fagen wasa tamaula a nahiyar Afrika da ma duniya.
Mamane Ada, sashen Hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.