logo

HAUSA

Don kare hakkin dan Adam ana bukatar gudunmowa maimakon takunkumi

2023-12-10 18:12:57 CMG Hausa

Yau ranar hakkin dan Adam ce. Shekaru 75 da suka gabata ne, aka zartas da sanarwar kare hakkin dan Adam a duniya yayin babban taron MDD, lamarin da ya haifar da babban tasiri kan kokarin al’ummar duniya na kare da raya hakkin dan Adam. Sai dai, abin takaici shi ne, yadda a wannan zamanin da muke ciki, a kan fake da batun “hakkin dan Adam” don biyan bukatu na siyasa.

Misali, kwanaki 2 da suka wuce, ma’aikatar kudi ta kasar Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu daidaikun mutane na kasashe 9, ciki har da Afirka ta tsakiya, da Kongo Kinshasa, da Sudan ta Kudu, bisa dalilin “keta hakkin dan Adam”. Kana a rana daya, kasar Amurka ita kadai ta kada kuri’ar kin amincewa a taron tattauna rikicin Isra’ila da Falasdinu na kwamitin sulhun MDD, inda ta sake hana ruwa gudu ga yunkurin kasashen duniya na neman tsagaita bude wuta a zirin Gaza. Wato kasar Amurka ta kakaba takunkumi na kashin kai kan wasu kasashe, da sunan “keta hakkin dan Adam”, yayin da a daya bangaren take goyon bayan kisan da ake yi wa fararen hular Falasdinu. Sannan kuma wai tana “taya al’ummar mutanen duniya murnar ranar kare hakkin dan Adam.

Sai dai, kowa na da 'yancin tabbatar da ra’ayinsa dangane da hakkin dan Adam. Lokacin da kasar Amurka da wasu kawayenta ke neman yin amfani da batun hakkin dan-Adam wajen dora wa wani laifi, da yanke hukunci, da sarrafa wasu kasasahe, da hana su samun ci gaba, za mu iya nuna akasin haka. Wato mu yi kokarin mai da hakkin dan Adam yadda ya kamata ya kasance, wanda ya kasance wani karfi dake haifar da ci gaba ga al’ummar dan Adam. A wannan fanni, wani rahoton da wasu kungiyoyin masana na kasar Sin suka fitar a kwanan baya, dangane da batun kare hakkin dan Adam, ya nuna wasu misalai.

Cikin rahoton an ayyana ci gaban zaman rayuwar jama’ar kasashen Afirka da aka samu ta hanyar hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin a kokarin aiwatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da kasar Sin ta gabatar. Misali, a lardin Bubanza na kasar Burundi, wani manomi mai suna Charles Ngendakumana, ya taba fama da talauci da yunwa. Sai dai daga bisani ya fara noman irin shinkafar zamani da aka tagwaita mai samar da yawan iri ko Hybrid, bisa taimakon da wani masanin ilimin aikin gona na kasar Sin ya samar. Bayan wasu shekaru 4, kudin shigar da ya samu ya ninka. Zuwa yanzu yana da yara 7, har ma ya gina wani sabon gida, gami da bude wani wurin sarrafa shinkafa. Wannan abu bai shafi kare hakkin dan Adam ba? Tabbas ya shafa. Wannan shi ne kare hakkin mutum na rayuwa.

Wani misali na daban da rahoton ya kunsa ya shafi tallafin da gwamnatin kasar Sin ta bayar da zummar taimakawa kauyuka dubu 10 dake nahiyar Afirka kama shirye-shiryen telabijin ta hanyar tauraron dan Adam. Zuwa karshen shekarar 2022, aikin ya amfani mutane kusan miliyan 10, na magidanta fiye da dubu 190, dake kauyuka 9512 na wasu kasashe 21 dake nahiyar Afirka. Wannan aiki ma ya shafi yunkurin kare hakkin dan Adam, inda ya samar da gudunmowa a fannin kare hakkin mutane na neman raya kansu.

Cikin rahoton an yi amfani da dimbin misalai irin wadannan, wajen bayyana wani daidaitaccen ra’ayi game da hakkin dan Adam, wato hakkin dan Adam na tushe shi ne neman rayuwa, daga baya za a nemi raya kai. Don haka ya kamata kasashe daban daban su yi kokarin hadin gwiwa don inganta harkokin tattalin arziki da na zaman al’umma, daga baya za a iya tabbatar da ci gaban harkokin hakkin dan Adam. Maimakon a yi ta sanya ido kan maganar “keta hakkin dan Adam” da saka takunkumi kan sauran kasashe, zai fi kyau a samar da hakikanin gudunmowa ga yunkurin kare hakkin mutane na rayuwa da raya kansu. A wannan zamanin da ake fuskantar dimbin kalubaloli a fannonin tsaro, da tattalin arziki, da muhalli, da dai sauransu, duniyarmu tana bukatar samun karin gudunmowa ta fuskar kare hakkin dan Adam maimakon takunkumi da yanke hukunci na kashin kai da a karshe ka iya shafar rayuwar bil-Adama.. (Bello Wang)