logo

HAUSA

Ingancin barci yana da nasaba da hadarin shan inna

2023-12-10 19:31:26 CMG Hausa

 

Masu karatu, yaya yanayin barcinku? Ko kuna yin minshari? Ko kuna shan wuya kafin yin barci? Ko ku kan farka daga barci a duhun dare? Ko kuna daukar tsawon lokaci kuna barci a tsakar rana? Ko kuna barci da yawa, ko kuma barci kalilan a rana guda? Masu nazari daga kasar Ireland sun yi nuni da cewa, ingancin barci yana da nasaba da hadarin shan inna.

Masu nazari daga jami’ar Galway ta kasar Ireland sun tantance bayanan mutane kimanin dubu 4 da dari 5, wadanda suka shiga nazarin da ya shafi kamuwa da cutar shan inna ba zato ba tsammani. Matsakaicin shekarunsu ya kai 62 a duniya. Wasu dubu 1 da dari 7 da 99 daga cikinsu ne suka kamu da cutar shan inna sakamakon raguwar jinni, ko karancin iskar oxygen a kwakwalwa. Wasu dari 4 da 39 ne suka kamu da cutar shan inna sakamakon zubar jini a kwakwalwa.

La’akari da shekarunsu da haihuwa, jinsi, da tarihinsu na fama da cututtuka, masu nazarin sun gano cewa, gwargwadon wadanda su kan dauki awoyi 7 suna barci a ko wane dare, wadanda matsakaicin tsawon lokacin barcinsu bai wuce awoyi 5 ba a ko wane dare, suna kara fuskantar barazanar kamuwa da cutar shan inna har sau 3. Wadanda su kan dauki awoyi fiye da 9 suna barci a ko wane dare kuma, irin barazanar da suke fuskanta ta karu da sau 1.

Shi kuma batun barci mai tsawo a rana fa? Masu nazarin sun ce, a kaucewa yin barci a rana fiye da awa 1, in ba haka ba, barazanar kamuwa da cutar shan inna za ta karu da kaso 88. Kana kuma, karuwar matsalolin barci na haddasa karuwar hadarin kamuwa da cutar shan inna.

Akwai wata alaka tsakanin yin barci maras inganci da kuma karuwar hadarin kamuwa da cutar shan inna. Ya kamata a sa muhimmanci kan ingancin barci yayin da ake kandagarkin kamuwa da cutar shan inna.

Ta yaya za a kyautata ingancin barci? Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing, ta kuma ba da shawarar cewa, a kwanta da wuri a tashi da wuri, har ma a lokacin hutu. A tabbatar da babu haske da kara a dakin kwana, kana kuma ba zafi ba sanyi. Kar a sa telebijin, kwanfuta da wayar salula a dakin kwana.

Ban da haka kuma, masu nazari daga sashen ilmin likitanci dangane da barci a jami’ar Harvard ta kasar Amurka sun shawarci cewa, kar a sha sinadarin caffeine, barasa ko nicotine awoyi 4 zuwa 6 kafin a yi barci. Idan ana son yin gajeren barci, ya fi kyau a yi barci kafin karfe 5 na yamma, kuma kar a yi barci mai tsawo. Kar a ci abubuwa a dab da yin barci. A sha ruwa kadan kafin a yi barci. A kyautata yin barci ta hanyar motsa jiki, amma kar a motsa jiki awoyi 3 kafin a yi barci. (Tasallah Yuan)