logo

HAUSA

Tsoffin Daliban Kenya Da Sin Sun Yi Murnar Cika Shekaru 60 Da Kulla Alaka Tsakanin Sin Da Kenya

2023-12-10 15:48:10 CMG Hausa

A jiya ne, mambobin kungiyar tsoffin daliban kasashen Kenya da Sin, suka gudanar da bikin murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen Kenya da Sin a Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

Bikin ya hallara 'yan kasar Kenya fiye da 100 da suka yi karatu a jami'o'in kasar Sin, inda aka gabatar da ayyuka da suka hada da wasan kwaikwayo da kide-kide na gargajiya na kasar Sin, da raye-raye, da ba da lambar yabo na wakoki ga tsofaffin daliban da suka yi fice a sassa daban daban na tattalin arziki, tare da nuna wani fim dake nuna nasarorin da aka cimma daga alakar dake tsakanin kasashen Sin da Kenya.

Mataimakin jakada kuma mai ba da shawara a ofishin jakadancin Sin dake kasar Kenya, Zhang Zhizhong ya bayyana cewa, 'yan kasar Kenya da suka yi karatu a kasar Sin, wata gada ce ta kyautata alaka a tsakanin kasashen biyu.

Shi kuwa shugaban kungiyar tsoffin daliban kasashen Kenya da Sin Henry Rotich, ya bayyana cewa, abokantaka tsakanin kasashen Kenya da Sin, wata shaida ce ta juriyar dangantakar abokantaka da ta shawo kan kalubale da kawo bunkasuwa ta hanyar hadin gwiwa, da mutunta juna, da neman cimma buri tare.

Rotich ya lura cewa, a cikin shekarun da suka gabata, tsofaffin daliban sun karu zuwa mambobi fiye da 1,500 kuma alama ce ta yadda 'yan Kenya suka yi imani da ingancin ilimi a kasar Sin. (Ibrahim)