logo

HAUSA

Sin ta bayyana matukar adawa da kin amincewar Amurka da kudurin tsagaita wuta domin jin kai

2023-12-09 16:42:56 CMG

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bayyana matukar takaicin kasar sa, game da yadda Amurka ta hau kujerar na ki, dangane da kudirin tsagaita wuta bisa yanayin jin kai a Gaza, wanda aka gabatar ga kwamitin tsaron MDD.

Kudurin, wanda hadaddiyar daular Larabawa ta mika daftarinsa ga zaman kwamitin tsaron MDD a jiya Juma’a, da goyon bayan kasashe sama da 100, ya samu amincewar kasashe 13 cikin mambobin kwamitin su 15, inda kuma Birtaniya ta kauracewa bayyana matsaya kan sa.

Game da hakan, Zhang Jun ya ce tashin hankalin dake gudana a Gaza, na haddasa mummunan yanayi na asarar rayuka da barnata dukiyoyi, kuma amincewa da wanzuwar halin da ake ciki, ya sabawa ikirarin kiyaye yanayin jin kai na al’ummar Gaza. Ya ce munafurci ne a rika maganar kare rayukan mata da kananan yara, a hannu guda kuma ana goyon bayan ci gaba da yaki.

Daga nan sai Zhang ya bayyana cewa, Sin na kira ga Isra’ila da ta saurari kiraye-kirayen sassan kasa da kasa, ta dakatar da kisan kan-mai-uwa-da-wabi da take yi kan al’ummar Gaza.  (Saminu Alhassan)