Tsohon firaministan Austria: Ra’ayin “raba gari ta fannin tattalin arziki” bai dace ba
2023-12-09 17:02:52 CMG Hausa
A kwanan baya, tsohon firaministan kasar Austria Wolfgang Schüssel, ya bayyana yayin wata hira ta musamman da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice cewa, ra'ayin "raba gari ta fannin tattalin arziki" bai dace ba.
Mista Schüssel, ya halarci taron kasa da kasa na "fahimtar kasar Sin" da aka yi a birnin Guangzhou na kasar Sin a kwanan baya, inda ya bayyana ra'ayinsa, game da gudanar da hadin gwiwa maimakon tayar da rikici tsakanin juna. A cewarsa, "dunkulewar duniya, da hadin gwiwar kasa da kasa, na da muhimmanci sosai ga samar da ci gaba, saboda yana taimaka mana wajen samun arziki, da wadata da gudanar da hadin kai cikin lumana."
Haka zalika, Mista Schüssel ya jaddada cewa, ra'ayin "raba gari ta fannin tattalin arziki" bai dace ba, domin zai sa mu zama matalauta. A cewarsa, asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya gudanar da wani bincike a lokacin bazara na bana, wanda ya nuna cewa, idan har da gaske kasar Amurka ta "raba gari ta fannin tattalin arziki" da Sin, yawan GDPn duniya zai yi hasarar da ta kai kashi 7 cikin dari, wanda ya zarce jimillar yawan asarar da aka samu, sakamakon matsalar kudi a tsakanin shekarun 2007 da 2008, da yaduwar annobar COVID-19. Don haka, ya ce, "raba gari ta fannin tattalin arziki" zai yi mummunan tasiri, kuma a ganin sa, hakan ba zai faru ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)