logo

HAUSA

An yabawa kasar Sin bisa inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa kan sauyin yanayi yayin babban taron sauyin yanayi na MDD

2023-12-09 18:02:31 CMG Hausa

A safiyar jiya Juma’a 8 ga watan nan ne kasar Sin ta gudanar da wani babban dandalin tattaunawa, kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, ta fuskar tinkarar sauyin yanayi, mai taken "zurfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa kan sauyin yanayi, da hada hannu da juna, don neman ci gaba ta hanyar rage gurbata iska".

A gun taron, wakilin musamman na kasar Sin kan batun sauyin yanayi Xie Zhenhua ya bayyana cewa, kasashe masu tasowa su ne suka fi fama da matsalar sauyin yanayi, kasancewar suna da rauni a fannin, da rashin samun isasshen tallafi. Ya ce, kasarsa na ci gaba da amfani da hanyar hada kai tsakanin kasashe maso tasowa, da nufin ba da taimakon zahiri ga sauran kasashe masu tasowa, don inganta sauye-sauyen makamashi, da inganta juriyar yanayi, da kuma inganta ci gaba ta hanyar rage gurbata iska.

Mahalarta taron sun yi tsokaci sosai kan kokarin da kasar Sin ta yi, da ma nasarorin da ta samu ta fuskar hadin gwiwar kasashe masu tasowa kan sauyin yanayi.

A nasa tsokaci, ministan albarkatun kasa da sauyin yanayi na kasar Malawi Michael Bizwick Usi, ya ce kasarsa na fuskantar kalubale iri-iri, inda sauyin yanayi ya haifar mata da aukuwar guguwa mai karfi a lokuta daban daban cikin shekaru biyu da suka gabata. Ya kara da cewa, “kasar Sin ta taimaka mana matuka, kana ta yi hadin kai da Malawi, wajen ganin an gina ababen more rayuwa, da hanyoyi, da sauran gine-gine a fannonin kiwon lafiya, da ilimi, wadanda suka dace da sauyin yanayi.”

Har ila yau, a yayin taron, kasar Sin ta rattaba hannu kan wata takardar aiki, game da hadin gwiwa tsakanin kasashe maso tasowa kan sauyin yanayi tare da kasar Chadi, da kuma wasu takardun shaida, na tabbatar da ayyuka game da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa kan sauyin yanayi, tare da manyan jami'ai daga ma'aikatar muhalli ta Botswana da wasu karin kasashen. (Mai fassara: Bilkisu Xin)