logo

HAUSA

COP28: Sin da Afirka za su bunkasa hadin gwiwa a fannin raya kananan ayyukan samar da makamashi mai tsafta

2023-12-09 16:50:54 CMG

An kaddamar da wani shirin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, wanda ke da burin ingiza gudanar da ayyukan samar da makamashi mai tsafta, a kanana da matsakaitan matakai. An kaddamar da shirin ne a jiya Juma’a a birnin Dubai na hadaddiyar daular Larabawa, a gefen tsaron sauyin yanayi na COP28 dake gudana.

An tsara cewa, shirin zai mayar da hankali ga bunkasa samar da lantarki daga kananan cibiyoyi, ta amfani da hasken rana nau’in “industrial photovoltaic ko PV, da na gas daga tsirrai ko “biogas” da sauran su.

Yayin bikin kaddamarwar, mataimakiyar shugaban kula da hadin gwiwar kasa da kasa kan batun yanayi a asusun kare muhalli da ke kasar Amurka Mandy Rambharos, ta ce kusan kaso 60 bisa dari na albarkatun makamashi da ake iya sabuntawa a duniya suna yankunan Afirka, sai dai kuma har yanzu ba a kai ga fara cin gajiyar su ba.

Jami’ar ta kara da cewa, hadin gwiwar samar da makamashi tare da Sin, zai iya zama hanyar sauya akalar da Afirka ke bi, wajen shawo kan karancin makamashi, da fita daga kangin fatara.

Rambharos, wadda kuma ta taba aiki a fannin sauya amfani da makamashi a kasar haihuwarta wato Afirka ta kudu, ta jinjinawa rawar da Sin ke takawa, duba da cewa Sin din ce ke samar da kaso 51 bisa dari, na jarin samar da makamashi mai tsafta a kasashen Afirka.  (Saminu Alhassan)