logo

HAUSA

Sinawa: Mutane Masu Kwazo Da Girmama Baki Da Ke Kallon Alkiblar Kawo Ci Gaba

2023-12-08 20:14:18 CMG Hausa

A kwanan nan na karanta wata tattaunawa da aka yi da hamshakin attajirin nan na duniya, shugaban kamfanin Tesla and Space X, Mista Elon Musk da yake bayyana cewa, "Na shafe lokaci mai yawa a kasar Sin kuma na sadu da shugabanni a lokuta da dama… yadda yawancin mutanen kasar suka kasance masu kaifin basira, da aiki tukuru na da matukar ban mamaki." in ji shi, kuma ya kara da cewa akwai mutane masu kaifin basira da dabara da aiki tukuru a kasar Sin fiye da na Amurka.

Wadannan kalaman nasa sun mayar da ni fagen waiwaye adon tafiya game da ziyarar da muka kai kasar Sin a ’yan shekarun baya.

Tun daga filin jiragen sama na Shanghai da muka sauka na shaida yadda Sinawa ke da kwazon aiki. Kowa ka gani babu wasa a bakin aikinsa kama daga jami’an tantance fasinjojin da suka shigo kasa har zuwa otel da za ka yi masauki.

Ziyarar da muka kai tashar teku mai zurfi ta Yangshan dake Shanghai ta sake bude min ido a kan kwazon Sinawa bisa yadda suka yi nisa wajen samar da ababen more rayuwa a kasarsu, musamman yadda suka gina gadar Donghai mai tagwayen titunan mota mai nisan kilomita 32.5 a saman teku. Sannan saman tudun da suka yi gine-gine a tashar ta Yangshan su ne suka samar da kusan kashi 90, tsibirin da suka cimma a wurin bai wuce kashi 10 ba.

Ko da yake, za mu iya cewa, gadar Donghai wasan yara ce idan aka kwatanta da gadar Danyang-Kunshan wacce ta sada wasu biranen lardin Jiangsu na kasar da a halin yanzu ita ce gada mafi tsayi a duk duniya, tana da nisan kilomita 164 (mil 104).

Bugu da kari, yanzu haka, sabo da kwazon aiki da Sinawa ke da shi, kididdiga ta nuna sun gina titunan mota tsawon kilomita miliyan 5.35 a fadin kasar. Misalan kwazon Sinawa ta fuskar tattalin arziki na nan birjik, ko ba komai zamowar Sin kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki ya isa shaida.

Da yake a zamanin nan, hankula sun karkata ga fannin bunkasa kimiyyar fasahar sadarwa, Sinawa ba a bar su a baya ba, limamai ne a wannan bangaren. Na gane wa idona abubuwa na ci gaban fasaha da kamfanin Huawei ke kerawa a lokacin da muka ziyarci reshensa na Shanghai. Kowace fasahar da aka samar walau aiki da jirgi mara matuki da fasahar 5G da birnin zamani wadda komai na’ura ke yi abubuwa ne na mamaki, amma babu wanda ya fi burge ni kamar wata fasahar kiwon shanu da Sin ta samar wadda manomi ke sanin halin da shanunsa ke ciki daga inda yake kwance ba tare da ya shigo cikin garke ba.

Sinawa na da kyakkyawan tsari a duk abin da suka sa a gaba kamar yadda muka gani a wuraren tarihin da muka ziyarta a Shanghai da Beijing irin su katafaren ginin Oriental Pearl Tower, babbar ganuwar Great Wall, fadar sarakuna ta Forbidden City, wurin bauta na Temple of Heaven da sauransu.

Ina da yakinin tsokacin da attajiri Elon Musk ya yi game da Sinawa a ’yan kwanakin nan za su tuna wa duk wanda ya taba ziyartar Sin da irin karamcin Sinawa da mamakin kwazonsu da ake koyar da su tun suna kanana kamar yadda na zama ganau ba jiyau ba.

Tabbas, tsare-tsare da kyakkyawar alakar da Sin ke ci gaba da kullawa da kasashen duniya don cin moriyar juna musamman mu a nan Afirka ta hanyar Dandalin Tattunawa na FOCAC, manuniya ce ga alkiblar da suka sa gaba ta kawo ci gaba ga duniya. (Abdulrazaq Yahuza)