logo

HAUSA

An gayyaci tsohon shugaban kasar Saliyo Koroma domin amsa tambayoyi kan yunkurin juyin mulki

2023-12-08 10:44:13 CMG HAUSA

 

’Yan sanda sun gayyaci tsohon shugaban kasar Saliyo Earnest Bai Koroma jiya Alhamis zuwa Freetown, babban birnin kasar, kan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba, a cewar sanarwar gwamnatin kasar.

“Da misalin karfe 11 na safiyar Alhamis agogon kasar, ’yan sandan Saliyo sun aika sammaci ga tsohon shugaban kasar Saliyo Dr. Ernest Bai Koroma, inda suka gayyace shi ya je hedikwatar hukumar binciken manyan laifuka dake Freetown cikin sa’o’i 24”, a cewar sanarwar da ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a ta fitar. “An gayyaci tsohon shugaban kasar ne domin ya taimaka wa ’yan sanda a binciken da ake yi kan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 26 ga watan Nuwamba a Saliyo."

Daga baya ofishin Koroma ya fitar da wata sanarwa, inda ya ce tsohon shugaban kasar Koroma zai yi tattaki daga Makeni, gari mai tafiyar sa'o'i uku zuwa Freetown, domin amsa gayyatar da aka yi masa. “A shirye nake na ba da taimako ga binciken ’yan sanda gaba daya. Dole ne mu  tabbatar da doka da oda a dimokaradiyyarmu,” a cewar Koroma a cikin sanarwar. (Muhammed Yahaya)