logo

HAUSA

Ya kamata kasashen Turai su kara fahimtar kasar Sin don karfafa dangantakar dake tsakaninsu

2023-12-08 11:09:19 CMG Hausa

A jiya Alhamis ne, aka kaddamar da taron shugabannin kasashen Sin da EU karo na 24 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A yayin ganawarsa da shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Turai Charles Michel da shugabar kungiyar tarayyar kasashen Turai Ursula von der Leyen, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata bangarorin biyu su tsaya tsayin daka, kan raya dangantakar abokantaka a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, da kara fahimtar juna, domin inganta dangantakar dake tsakaninsu da zuciya daya.

A nasu bangare, shugabannin kasashen Turai sun ce, ba su son neman raba-gari da kasar Sin, kuma sun yi imanin cewa, bunkasuwar kasar Sin cikin dogon lokaci ba tare da tangarda ba ta dace da moriyar kasashen Turai.

A cewar wasu manazarta, Sin da EU sun aike da wani sako mai kyau don tinkarar kalubale ta hanyar yin shawarwari da hadin gwiwa, wanda ya dace a yi maraba da shi.

A bana ake cika shekaru 20 da kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasar Sin da EU, yadda bangarorin biyu suka raya dangantakar dake tsakaninsu cikin shekaru 20 da suka gabata, ya nuna cewa, idan aka dauki juna a matsayin abokai, aka kuma martaba juna, to, tabbas, huldar dake tsakaninsu za ta kara bunkasa. A cikin shekaru 20 masu zuwa, akwai bukatar bangarorin biyu su kara fahimtar juna, da daga huldar dake tsakanin Sin da Turai zuwa wani sabon matsayi, a lokacin da suke dukufa wajen inganta zamanintarwar kasar Sin da dunkulewar kasashen Turai tare. Hakan ba wai kawai zai amfanar da jama'ar bangarorin biyu ba, har ma zai kawo karin kwanciyar hankali da tabbaci ga duniya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)