logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun bayyana nadama game da hari ta sama bisa kuskure da ya kashe mutane 85

2023-12-08 09:53:04 CMG HAUSA

 

Rundunar sojin Najeriya, ta bayyana nadama game da wani hari ta sama bisa kuskure da sojoji suka kai a wani kauye a jihar Kaduna dake yankin arewacin kasar a farkon wannan mako, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 85.

Mai magana da yawun rundunar, Edward Buba ya shaidawa manema labarai a Abuja, babban birnin kasar cewa, sojojin Najeriya sun koyi darasi daga hadarin da ya faru, sun kuma yi alkawarin inganta kwarewarsu, tare da ci gaba da gudanar da ayyukansu, kamar yadda dokoki da ka’idojojin aikin soja na kasa da kasa suka tanada.

Idan ba a manta ba, a yammacin ranar Lahadin da ta gabata ce dai, sojoji suka kaddamar da wani hari ta sama a jihar Kaduna, yayin wani samame na yaki da ta’addanci, amma suka afkawa wani yanki da fararen hula ke zaune bisa kuskure, inda suka kashe fararen hula a kalla 85 tare da jikkata wasu 66.

Erward Buba ya tabbatar da cewa, sojojin sun koyi darasi bisa ga abubuwan da suka faru, kuma za su ci gaba da yin gyare-gyare yayin tafiyar da ayyukansu. Yana mai cewa, yanzu dai abu ya riga ya faru, kuma kamar yadda na ambata a takaice, “mun kuduri aniyar shawo kan lamarin yadda ya kamata.”

Ya kuma yi watsi da rade-radin cewa, rashin hadin kai tsakanin jami’an tsaro ne ya haifar da wannan barna. Ya ce ana gudanar da ayyukan soji a fadin kasar baki daya, tare da sojoji, na ruwa, da na sama.

Jami'in sojan ya ce, za su inganta ka'idoji da tsare-tsaren ayyukansu, yana mai ba da tabbacin kaucewa aukuwar irin wadannan abubuwa a nan gaba.

Wata sanarwar da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar na bayyana cewa, tun da farko dai rundunar sojin Najeriya ta amince da aikata kuskure, a wata ganawra da ta yi da jami'an gwamnati a ranar Litinin. (Ibrahim Yaya)