logo

HAUSA

Kamata Ya Yi Kasashe Masu Wadata Sun Cika Alkawarin Da Suka Yi Na Samar Da Kudaden Taimakawa Kasashe Masu Tasowa Wajen Tinkarar Sauyin Yanayi

2023-12-08 09:46:27 CMG HAUSA

DAGA MINA

Taron COP28 na cimma matsaya daya wajen kaddamar da asusun biyan asarar sauyin yanayi don taimakawa kasashe masu tasowa wajen tinkarar matsalar sauyin yanayi. AL da Jamus na yi alkawarin samar da kudin dalar miliyan 100 kowanensu, yayin da adadin Birtaniya ya kai dalar miliyan kimanin 50. Amma Amurka wadda ta kan bayyana mata a matsayin kasa dake matukar sauke nauyin dake wuyanta wajen tinkarar wannan matsala, ta samar da dalar miliyan 17.5 kawai, kuma yawan hayaki mai dumamma yanayi da ta fitar gaba daya ya kai koli a duniya.

Amurka da dai sauran kasashen yamma sun kwashe shekaru fiye da dari suna raya masana’antu, abin da ya baiwa musu arziki da bunkasuwar tattalin arziki mai wadata, amma a sa’i daya, sun yi amfani da makamashi da albarkatu mafi yawa tare da fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da yawa, hakan ya sa dole ne wadannan kasashe sun dauke alhakin bullowar matsalar sauyin yanayi. Rahotanin da MDD ta bayar na nuna cewa, tun lokacin da aka yiwa masana’antu kwaskwarima, kashi 58% na yawan abubuwan dumamman yanayi da bil Adama suka fitar na kafin kafin shekarar 1990, daga shekarar 1850 zuwa 2019, yawan iskar Co2 da nahiyar arewacin Amurka da Turai suka fitar ya kai kashi 23% da 16% na dukkan duniya. Amma, kasashe maso tasowa ne suke fama da illar da sauyin yanayi ke haifarwa, wanda ya kasance rashin daidaito a fannin yanayi. Shugaban COP28 Dr. Sultan Al Jaber ya ce, wasu kasashe maras karfi musamman ma tsibiran kasashe da kasashe mafi maras karfi suna fama da illar sauyin yanayi mai tsanani.

Kamata ya yi, kasashe masu wadata sun sauke nauyin dake wuyansu na samar da kudade don taimakawa wadannan kasashe wajen tinkarar matsalar sauyin yanayi, don samar da daidaici da adalci a fannin yanayi, ciki hadda tattare kudade don taimakawa wadannan kasashe da kaddamar da asusun biyan asarar sauyin yanayi. Bai kamata, kasashe masu tasowa sun yi asara saboda bunkasuwa da wadatar da kasashe masu wadata suke samun. (Mai zana da rubuta: MINA)