logo

HAUSA

AU da hukumomin MDD sun bukaci daukar matakan gaggawa don kawo karshen matsalar yunwa a Afirka

2023-12-08 10:09:14 CMG HAUSA

 

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) da hukumomin MDD sun yi kira da a dauki matakin gaggawa, don kawo karshen matsalar yunwa a nahiyar Afirka, inda kusan mutane miliyan 282, ko kimanin kashi 20 cikin 100 na al'ummar nahiyar, ke fama da karancin abinci mai gina jiki.

Hukumar samar da abinci da aikin noma ta MDD (FAO), da Hukumar Tarayyar Afirka, da Hukumar MDD mai kula da Tattalin Arziki, da shirin samar da abinci na duniya (WFP), sun bayyana a cikin wani rahoton hadin gwiwa cewa, adadin mutanen da ke fama da karancin abinci mai gina jiki ya karu zuwa miliyan 57, tun bayan barkewar cutar COVID-19.

Hukumomin sun bayyana a cikin rahoton mai taken “bayani kan alkaluman samar da abinci da abinci mai gina jiki na shekarar 2023 a shiyyar Afirka” gami da halin da ake ciki cewa, kiran da ake yi na kara daukar matakai gaskiya ne, bisa la'akari da yadda ake hasashen samun raguwar bunkasuwar tattalin arzikin duniya, ga hauhawar farashin kayayyaki baki daya, da hauhawar kudin ruwa na lamuni a kasuwannin cikin gida da na kasa da kasa tun daga shekarar 2022.

Hukumomin sun ce, kimanin kashi 78 cikin 100 na galibin al'ummar Afirka, ko kuma fiye da mutane biliyan 1, ba su iya cin abinci mai kyau, idan aka kwatanta da kashi 42 cikin 100 na al’ummar duniya, kuma adadin karuwa yake. (Ibrahim Yaya)