logo

HAUSA

Ba za a cimma wannan yarjejeniya ba tare da taimakon Sin ba

2023-12-08 07:18:44 CMG HAUSA

 

Daga ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa 12 ga watan Disamba na shekarar 2023, an gudanar da babban taron kasashen duniya masu sa hannu kan yarjejeniyar tsarin MDD kan sauyin yanayi karo na 28 COP28 a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa. Taron ya kuma yi takaitaccen bayani kan yadda ake aiwatar da yarjejeniyar Paris

Manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron tare da gudanar da wasu ayyuka.

A shekarar 2015, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron MDD kan sauyin yanayi a Paris, inda ya gabatar da tunani da matsayin Sin kan yadda za a daidaita matsalar sauyin yanayi a duniya, tare da kara azama kan cimma daidaito kan yarjejeniyar ta Paris.

Shugaban babban taron sauyin yanayi na Paris a waccan lokaci Laurent Fabius ya ce, idan babu goyon baya mai yakini da shugaban Sin ya baiwa yarjejeniyar, ba za a kaiwa ga cimma matsaya daya kan wannan yarjejeniyar ba. Laurent Fabius ya taba ganawa da shugaba Xi Jinping sau da dama a baya, inda ya ce, kauna da hangen nesa da shugaba Xi Jinping yake da su game da kasarsa sun burge ni matuka, abin da shugabannin kasashen yamma ke karanci. (Amina Xu)