logo

HAUSA

Kamfanin Sin ya kammala bangare na biyu na aikin gina yankin masana’antu na kasa da kasa a Senegal

2023-12-07 14:15:57 CMG HAUSA

 

Kashi na biyu na aikin yankin masana’antu na kasa da kasa na Gamuniyaju, wani aikin ba da misali ne na manyan dabarun raya kasar Senegal. A ran 5 ga wata bisa agogon wurin ne, aka yi bikin kammala kashi na biyu na aikin gina wannan yankin masana’antu da kamfanin Sin ya yi.

A cikin jawabin da ya gabatar yayin bikin, shugaban kasar Senegal Macky Sall ya ce, ya yi amfani da wannan dama, wajen mika godiyarsa ga daukacin abokan dake taimakawa kasarsa a fannonin fasaha da kudade wajen raya masana’antun Senegal, kuma yana matukar jinjinawa hadin kan dake tsakanin kasashen Sin da Senegal.

Jimillar fadin gine-gine a kashi na biyu na yankin masana'antu na kasa da kasa na Gamuniyaju ta kai murabba’in mita dubu 95, kuma wani kamfanin kasar Sin ne ya fara wannan aiki ne a watan Disamban shekarar 2021. Ana sa ran aikin zai samar da guraben ayyukan yi sama da dubu 4 a kasar Senegal, matakin da zai taimaka wa kasar ta Senegal wajen warware matsalolin da suka hada da rashin guraben aikin yi da ma raunin masana'antu. (Amina Xu)