logo

HAUSA

Wakilin Sin ya bukaci a kara ba da taimakon jin kai kan batun Ukraine

2023-12-07 10:40:24 CMG Hausa

Jiya Laraba, kwamitin sulhu na MDD ya kira taron kan yanayin da ake ciki a kasar Ukraine. A jawabinsa, wakilin kasar Sin ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su kara kaimi wajen bayar da taimakon jin kai. Ya kuma jaddada cewa, matsayin kasar Sin kan batun kasar Ukraine bai canja ba, kasar Sin tana goyon bayan bangaren dake neman shimfida zaman lafiya, da yin shawarwari, kasar Sin tana fatan shimfida zaman lafiya a yankin ta hanyar yin shawarwari, da hanzarta tsagaita bude wuta gaba daya.

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Geng Shuang ya bayyana cewa, ci gaba na yake-yake a kasar Ukraine ya lalata manyan ababen more rayuwa da dama dake cikin kasar, kuma ana samun tafiyar hawainiya wajen gyara su. A baya-bayan nan, kasashen Ukraine da Rasha da ma wasu kasashen yankin Bahar Maliya, sun fuskanci matsanancin yanayi da saukar dusar kankara da ba kasafai ake samu ba, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin sufuri da wutar lantarki da kuma haddasa asarar rayuka, kasar Sin ta damu da hakan. Don haka, kasar Sin tana kira ga gamayyar kasa da kasa da su kara ba da taimakon jin kai ga kasashen da abin ya shafa, ta yadda jama’ar dake zaune a yankuna masu fama da yake-yake, za su zauna lafiya cikin wannan yanayin sanyi mai tsanani.

Ya kara da cewa, bisa hasashen da aka yi, an ce, tattalin arzikin duniya zai ci gaba da fuskantar tafiyar hawainiya a shekara mai zuwa, kuma zai kasance mafi karancin ci gaba tun daga shekarar 2020. Daya daga cikin muhimman dalilan shi ne, mummunan tasirin rikice-rikicen shiyya-shiyya. Ci gaban yin yaki a kasar Ukraine bai dace da moriyar ko wane bangare ba, ya kamata gamayyar kasa da kasa su hada kai domin rage mummunan tasirin da yakin kasar Ukraine ya haifarwa sauran kasashen duniya, da kare tsaron abinci, da makamashi da hada-hadar kudade, ta yadda za a tabbatar da aiwatar da harkokin saya da sayarwa a tsakanin kasa da kasa yadda ya kamata. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)