logo

HAUSA

An fara aiki da cibiyar buga muhimman takardu ta AU da Sin ta ba da taimakon ginawa

2023-12-07 14:14:04 CMG HAUSA

 

A ran 5 ga wata, bisa agogon wurin, an kaddamar da cibiyar buga muhimman takardu ta kungiyar Tarayyar Afirka wato AU da kasar Sin ta ba da taimakon ginawa. Mataimakiyar shugaban hukumar gudanarwar AU Monique Nsanzabaganwa, ta bayyana godiya ga hadin kai na dogon lokaci dake tsakanin Sin da AU.

A wannan rana kuma, Monique Nsanzabaganwa ta bayyana a bikin cewa, wannan cibiyar ta kasance wani muhimmin bangare na aikin yi wa AU kwaskwarima da zamanintar da AU. Ta kuma bayyana godiyarta ga taimako da goyon baya da Sin take nunawa AU, wannan cibiyar ta bayyana ci gaba mai inganci da aka samu daga bunkasuwar huldar abokantaka da hadin kai.

Wannan cibiyar ta buga muhimman takardu tana hedkwatar AU, kuma gwamantin Sin ce ta samar da na’urorin dake cibiyar kyauta, da ma tura kwararru don ajiye da gwada na’urori da kuma ba da horo. Fara aiki da wannan cibiyar na bayyana cewa, AU na da kamfanin kanta na buga muhimman takardu.(Amina Xu)