FIFA: Argentina ce kan gaba a kwallon kafa
2023-12-07 21:02:49 CMG Hausa
Kasar Argentina, wadda ke da kofin kwallon kafa na duniya har guda 3, ita ce kan gaba a teburin hukumar FIFA, a jerin kasashe mafiya kwarewa a fannin taka leda, yayin da ita kuma Ingila ta matsa sama zuwa jerin kasashe 3 dake sahun gaba a duniya, kamar dai yadda FIFA din ta bayyana a karshen makon jiya.
FIFA ta ce Argentina ta kare matsayin da take kai da maki 1855.20, sai kuma Faransa a matsayi na 2. Yayin da rashin nasarar da Brazil ta yi hannun Colombia da Argentina, ya fitar da Brazil din daga jerin 3 na farko a jadawalin, inda a yanzu ta sauka zuwa matsayi na 5.
Ingila ta daga zuwa matsayi na 3, yayin da Belgium ke biye a matsayi na 4. Sauran kasashen dake saman teburin sun hada da Netherlands, wadda ta daga zuwa matsayi na 6, sai kuma Portugal, da Sifaniya, da Italiya da Croatia dake jerin goman farko.
A watan Nuwamban bana, an gudanar da jimillar wasannin kasa da kasa har 188, a wani bangare na fitar da guraben buga gasar cin kofin duniya na shekarar 2026 a nahiyoyin Afirka, da Asiya da Kudancin Amurka.
Tsaffin ‘yan kwallon Kamaru sun doke takwarorin su na Najeriya
Yayin wasan kwallon kafa na tsofaffin ‘yan kwallon Kamaru da Najeriya da aka buga a Alhamis din makon jiya, kungiyar Kamaru ta doke ta Najeriya da ci 3 da 1.
An dai buga wasan gaban ‘yan kallo sama da 10,000 a filin wasa na Omnisport dake kusa da garin bakin ruwa na Limbe. Yayin wasan, Julius Aghahowa ne ya ciwa Najeriya kwallo daya tilo da ta samu, karkashin tawagar da Jay-Jay Okocha ya jagoranta.
A bangaren Kamaru kuwa, ‘yan wasan kasar Samuel Eto'o, da Bernard Tchoutang da Ndip Tambe ne suka zura kwallaye a ragar Najeriya, a wasan da ya yi kama da na cin kofin Afirka na shekarar 2000, lokacin da kasashen biyu suka fafata, kuma Kamaru ta doke Super Eagles ta Najeriya da ci 3 da 1, ta bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan sun tashi wasa kunnen doki ci 2 da 2.
Game da yadda wasan ya gudana, wani dan Najeriya da ya kalli wasan mai suna Emeka James, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa "Wasan ya kayatar, kuma da an tashi kunnen doki, an kuma buga fenareti, da zai sakamakon ya yi daidai da na wasan karshe na shekarar 2000 da kasashen 2 suka taba bugawa. A gani na wadannan ‘yan wasa za su iya ma buga kwallo a gasar zakarun turai ta yanzu".
A nasa bangare kuwa, wani mai goyon bayan Kamaru Michael Jaaba, ya ce yana cike da farin cikin ganin ‘yan wasa irin su Samuel Eto'o da Jay-Jay Okocha. A cewar sa "Ba su ba ni kunya ba. Mun nishadantu da wannan wasa na sada zumunta".
Kasar Kamaru ce ta shirya wasan, a wani bangare na ayyukan da aka tsara domin bikin murnar samun amfanin gona da ake yiwa lakabi da “Plantain Festival”.
Morocco da Portugal da Sifaniya sun gabatar da bukatar karbar bakuncin kofin kwallon kafa na duniya na 2030
Hukumar kwallon kafa ta kasa da kasa FIFA, ta sanar da karbar yarjejeniyar hadin gwiwa, na kasashen Morocco da Portugal da Sifaniya, game da burin su na karbar bakuncin gasar cin kofin duniya na shekarar 2030 dake tafe.
A daya hannun, su ma kasashen Uruguay, da Argentina da Paraguay, sun tabbatar da amincewar su, ta neman a basu damar karbar bakuncin hadin gwiwa na gasar ta 2030.
Har ila yau, ita ma Saudiyya ta mika bukatar neman karbar bakuncin gasar ta hukumar FIFA, amma ta shekarar 2034. Ana kuma sa ran a nan gaba, majalissar gudanarwar FIFA za ta zartas da hukunci kan wadannan bukatu.
A watan Janairun shekarar 2024 dake tafe ne, FIFA za ta gudanar da zaman tattaunawa da daukacin masu neman karbar bakuncin gasannin na kasa da kasa, kana za ta wallafa rahoton ta na tantancewa bayan yin cikakken nazari.
Guerrero na shawarar tsawaita kwangila a LDU Quito
Tauraron kwallon kafa na kungiyar LDU Quito ta Ecuado Paolo Guerrero, na shawarar tsawaita kwangilar sa a kungiyar da yake bugawa wasa da shekara guda, bayan da kungiyar ta bayyana bukatar hakan.
Dan wasan mai shekaru 39 da haihuwa dan asalin kasar Peru, ya ciwa LDU Quito kwallaye 8 a wasanni 18 da ya buga mata, bayan dawowarsa kulaf din a watan Yuli, don buga wasa na watanni 6. Kwallayen da ya ciwa LDU Quito sun baiwa kulaf din damar lashe kofin “Copa Sudamericana”, inda a wasan karshe suka doke kungiyar Fortaleza ta Brazil, a ranar 28 ga watan Oktoban da ya gabata.
Yayin wata zantawa da kafar radio ta FB, daraktan LDU Quito mista Esteban Paz, ya ce "Mun riga mun mikawa Paolo Guerrero bukatar mu a hukumance, kuma muna fatan zai amince ya zauna tare da mu. Mun tattaunawa da wakilan sa, amma ba wanda zai yanke hukuncin karshe sai shi kan sa Paolo. Shi kadai ne ya san ko a shekarun sa 39 ko 40 zai iya ci gaba da kwallo ko a’a, amma dai mu mun bayyana bukatar ya ci gaba da kasancewa tare da mu".
Baya ga kungiyar LDU Quito da yake bugawa wasa, Paolo ne dan wasa mafi ci wa kasar Peru kwallaye a tarihi, inda ya ciwa kasar ta sa kwallaye 39 cikin wasannin kasa da kasa 114 da ya bugawa Peru. Cikin shekaru 21 da ya shafe yana taka leda a ajin kwararru, Paolo ya buga wasa a kungiyoyin Bayern Munich, da Hamburg, da Corinthians da Flamengo.
Shugaban IOC ya jinjinawa kokarin birnin Paris na kawata kauyen gasar Olympic ta 2024
Shugaban kwamitin shirya gasar Olympic na kasa da kasa ko IOC, mista Thomas Bach, ya jinjinawa aikin da ya gani a kauyen wasannin Olympic na birnin Paris, yana mai cewa, birnin ya yi rawar gani wajen gudanar da shirye shirye masu kayatarwa, na tunkarar gasar Olympic dake tafe a shekarar 2024. Mista Bach ya bayyana hakan ne bayan ran gadi da ya gudanar a kauyen wasannin dake Seine Saint-Denis department, wanda ke arewa da tsakiyar birnin Paris.
Bach da sauran mambobin babban kwamitin IOC, sun kammala ziyarar kwanaki 4 a Paris, inda suka yi ganawar karshe da helkwatar kwamitin shirya gasar Olympic ta Paris, kana suka ziyarci kauyen gasar dake kusa da helkwatar.
Yayin da yake zantawa da manema labarai, mista Bach ya ce "Abun faranta rai ne ganin yadda kauyen Olympic ya kusa kammala, kuwa tabbas da zarar an gama gasar, za a ji yadda ‘yan wasa za su rika labarin sa.
Ya ce "Wannan ne wurin da zai kasance zuciyar Olympic, kuma ‘yan wasa za su samu wurin zama mai inganci. Daga abun da muka gani a nan wurin yana da kayatarwa, ga kyan gani"
A nasa tsokacin kuwa, shugaban kwamitin tsare tsare Tony Estanguet cewa ya yi "An kusa kammala aikin kauyen na Olympic, kuma za a mika shi ga IOC a farkon watan Maris na badi, domin kwamitin tsare tsare ya samu damar shirya karbar ‘yan wasan da za su fara hallara, tun daga ranar 15 ga watan Yuli".
An tsara gudanar da gasar Olympics din na badi ne tsakanin 26 ga watan Yuli zuwa 11 ga watan Agusta, kana a gudanar da ajin gasar na masu bukata ta musamman daga ranar 28 ga Agusta zuwa 8 ga Satumba.
Kauyen wasan da aka samar, zai kunshi rukunin gidaje 2,800, wadanda kaso 25 bisa darin su na sayarwa ne, yayin da sauran za a bayar da su haya.
Mista Estanguet ya ce bana akwai ayyuka da dama da za a gudanar masu nasaba da gasar dake take, ciki har da sayar da tikiti, da tsara ayyukan sa kai, da gwaje gwajen ayyuka, wadanda dukkanin su ke bukatar shirye shirye masu sarkakiya.
Ya ce rahoton shirye shiryen gudanar da gasar ta Paris 2024, na kunshe da muhimman bangarori 3, da suka hada da gudanarwa, da kasafin kudi, da tsara tattaunawa.
Gasar dai na da abokan hulda 55 na cikin gida. A baya bayan nan kuma, an fitar da tikiti 400,000 domin sayarwa masu sha’awar kallon ta, inda kuma cikin sa’a daya, aka sayar da tikiti har 380,000, wanda hakan ke nuna cewa ya zuwa yanzu, an sayar da tikitin gasar har miliyan 7.5, ciki jimillar tikiti miliyan 10 da za a sayar domin kallon gasar ta Olympic.
A cewar mista Bach, taron ganawa da suka yi, da kuma rahoton da hukumar tsare tsare ta IOC ta fitar, ya kara tabbatar da cewa, birnin Paris ya shirya tsaf domin gudanar da gasar ta badi cikin nasara.