An fitar da sanarwar “fasahar sadarwa dake goyon bayan dauwamammen ci gaban kasashen dake bin shawarar ‘ziri daya da hanya daya’”
2023-12-07 10:42:09 CMG Hausa
Jiya Laraba, aka bude taron dandalin tattaunawa kan fasahohin sadarwa na zamani na duniya kan “Ziri daya da hanya daya” na shekarar 2023 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Wakilai sama da guda 100 daga kasashe da kungiyoyin kasashen duniya guda 33 sun halarci wannan taro mai taken “Fasahar sadarwar duniya da neman dauwamammen ci gaban kasa da kasa”.
Taron da aka gudanar bisa hadin gwiwar kungiyar nazarin ilmin fasahar sadarwar duniya, da cibiyar nazarin bayanai kan dauwamammen ci gaba ta duniya da kuma kwalejin nazarin bayanan sararin samaniya na jami’ar kimiyya da fasahar kasar Sin, ya tattauna kan yadda kasashen dake cikin shawarar “ziri daya da hanya daya” suke raya fasahohin sadarwa a halin yanzu da kalubalolin da suke fuskanta a wannan fanni. Kana, wakilan sun tattauna kan babban gudummawar da fasahar sadarwar duniya za ta samarwa kasashen dake shawarar “ziri daya da hanya daya” wajen neman dauwamammen ci gaba kan fannonin dake shafar muhallin halittu, da fuskantar matsalar sauyin yanayi, da rigakafin aukuwar hadurra, da kula da yankunan gabar teku, da binciken hadurran tsaunuka da dai sauransu.
A yayin taron wakilai daga kasashen dake shawarar “ziri daya da hanya daya” guda 20 da suka hada da kasashen Iran da Kazakhstan da Malaysia da Mongoliya da Nepal da sauransu, sun zartas da sanarwar “fasahar sadarwar duniya na goyon bayan dauwamammen ci gaban kasashen dake cikin shawarar ‘ziri daya da hanya daya’”. Lamarin da ya nuna cewa, kasashen sun sami gagarumin ci gaba kan hadin gwiwar fasahar sadarwar zamani ta duniya a fannoni daban daban, wadda za ta yi muhimmin tasiri ga kasashen wajen cimma burinsu na samun dauwamammen ci gaba. (Mai fassarawa: Maryam)