logo

HAUSA

Cibiyoyin ilimi na Sin da Habasha sun amince da bunkasa kwarewa a fannin fasaha

2023-12-07 10:08:16 CMG Hausa

Jami'ar koyon ilimi da fasaha ta Tianjin dake kasar Sin (TUTE), da cibiyar koyar da fasaha da sana'o'i ta kasar Habasha (TVTI) sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa, don bunkasa kwarewar sana’o’i da ke mai da hankali kan ci gaban fasaha.

Yarjejeniyar wacce aka sanya hannu a kai ranar Talata, a yayin wani taron karawa juna sani da cibiyar koyar da sana’o’i ta Luban dake Habasha wadda kasar Sin ke daukar nauyinta ta shirya a harabar gidan talabijin na TVTI dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, ta yi hasashen kara inganta ayyukan koyar da sana’o’i a cibiyar Luban dake Habasha.

A yayin bikin, babban darekta na TVTI, Biruk Kedir, ya bayyana cewa, yarjejeniyar ta kasance wani kyakkyawan misali, na yadda kasar Sin ke kokarin inganta ilmin fasaha da injiniya a kasar dake gabashin Afirka.

Kedir ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, bangarorin biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar karfafa hadin gwiwarsu, ta hanyar cibiyar horas da sana’o’i ta Luban, wani muhimmin dandali na taimakawa Habasha wajen cike gibin da ke akwai a wannan fanni. (Ibrahim Yaya)