logo

HAUSA

Babu wata shaida da ta nuna cewa an tilastawa ma’aikata yin aiki a kamfanin Volkswagen na Xinjiang

2023-12-07 18:23:35 CMG Hausa

Wasu masu binciken kudi na waje da kamfanin kera motoci na Volkswagen na kasar Jamus ya yi hayarsu, sun bayyana cewa, ba su samu wata shaidar dake nuna cewa, an tilastawa ’yan kwadago yin aiki a kamfanin dake jihar Xinjiang ta Uygur ta kasar Sin ba. Rahoton da MSCI ESG ya wallafa mai kunshe da zarge-zargen take hakin bil Adama a jihar Xinjiang, "ba daidai ba ne, kuma baki dayansa yaudara ce."