logo

HAUSA

Sin na ba da gudummawa ta fuskar ingiza zamanantar da duniya

2023-12-07 16:25:37 CMG Hausa

Yayin da duniya ke ci gaba da fuskantar manyan kalubale daga sassa daban daban, masharhanta na ganin wannan lokaci ne da ya dace sassan kasa da kasa su kara azamar bullo da dabarun hadin gwiwa, na tsame duniya daga mawuyacin halin koma bayan tattalin arziki da zamantakewa da take ciki.

Kaza lika, lokaci ya yi da duniya za ta rungumi matakan wanzar da zaman lafiya, da samar da ci gaban bai daya, domin cin gajiyar dukkanin al’ummun kasa da kasa. Hakan ne kuma ya sa har kullum kasar Sin ke sahun gaba a wannan fage. Idan mun lura da matakan da Sin ke dauka na baiwa ci gaban duniya gudummawa, za mu gamsu cewa matakai ne masu fa’ida ta kyakkyawan tasiri, ta yadda har kullum Sin din ke aiki tukuru, kuma kafada da kafada da sauran sassan duniya, wajen ganin an cimma burin zamanantar da al’amura, da samar da ci gaba cikin lumana, da aiwatar da matakan hadin gwiwa na bai daya.

Sanin kowa ne cewa, duniya gida ne guda na daukacin bil Adama, kuma wuri na cin gajiyar daukacin al’ummun kasashen duniya, don haka kamata ya yi sassan kasa da kasa su kara kokarin yin hadin gwiwa, wajen shawo kan kalubalen dake addabar duniya, su goyi bayan matakan bunkasa duniya na bai daya, da inganta moriyar jama’a baki daya.

Idan muka yi la’akari da ci gaban da kasar Sin ke samu ta fuskar zamanantar da kasa, da fadada bude kofa bisa babban matsayi, da ma yadda kasar ke kara azamar bunkasa ci gaba mai inganci, za mu fahimci sirrin dake cikin damammaki da kasar ke samarwa, wajen ingiza ci gaban duniya.

Tsarin zamanantar da kasa na Sin, yana ci gaba da ingiza bunkasar tattalin arzikin duniya, kuma sabanin makamantansa da ake aiwatarwa a yanukunan yammacin duniya, salon kasar Sin na bayar da damar samun ci gaban bai daya. Tuni kasar Sin ta cimma manyan nasarori a fannin yaki da fatara, da kyautata rayuwar al’ummarta. Bisa hakan, muna iya cewa, salon zamanantarwa na Sin ya dace da burin daukacin bil Adama na samun ingantacciyar rayuwa.

Yayin da Sin ke shiga sabon mataki na ci gaba mai inganci, kofofin takara mai tsafta suna kara budewa, kuma tsarin kasar na bude kofa ga kowa, da ingiza ci gaban bai daya, da gudummawarta a fannin gina budadden tsarin tattalin arzikin duniya, kyakkyawan labari ne ga duniya da a yanzu ke fama da tafiyar hawainiya a fannin na tattalin arziki.

Fatan dai shi ne duniya ta kara fahimtar kasar Sin, a matsayinta na abokiyar tafiya, ba wai barazana ko abokiyar hamayyar ko wane bangare ba. (Saminu Hassan)