logo

HAUSA

Yadda Za A Rage Illar Da Sauyin Yanayin Duniyarmu Ke Kawo Wa Bil Adama

2023-12-06 07:56:37 CMG Hausa

Yanzu haka kasashe da ragowar bangarorin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD, sun hallara a birnin Dubai na hadaddiyar daular Larabawa, inda suke gudanar da taro kan sauyin yanayi ko COP28, inda shugabannin kasashen duniya suke tattauna matsalolin dake hana ruwa gudu game da magance matsalar sauyin yanayi dake ci gaba da addabar sassan duniya ta fannoni daban-daban.

Hasali dai yawan iskar gas da carbon na asali a cikin yanayi ta zahiri, a dalilin rashin komawar zafin rana sararin samaniya shi yake haifar da zafin yanayi, daga bisani kuma ayyukan dan Adam da suka hada da konewar burbushin halittu, sare dazuzzuka da kona su da kuma noma musamman kiwon dabbobi suna kara yin tasiri ga yanayi da zafin duniya. Amma sinadaran carbon dioxide (CO2), methane, nitrous oxide, Gas mai fluorine sune akan gaba wajen dumamar yanayi, musamman carbon dioxide (CO2) shi yafi bada gudummawa ga dumamar yanayi.

La’akari da hakan ne a watan Satumba na shekarar 2020, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin na da burin kawar da sinadarin carbon dioxide kafin shekarar 2030, da kuma cimma matsaya game da kawar da iskar carbon gaba daya kafin shekarar 2060.

Hanyoyin magance matsalar sauyin yanayi sune kaucewa abubuwan da ke dumama yanayi, wato rage yin amfani da makamashi masu fitar da iska ko hayakin carbon mai gurbata muhalli, a koma amfani da makamashi mai tsafta kamar makamashi da ake samu daga hasken rana da karfin iska da ruwa wanda tuni kasar Sin ta shige gaba a wannan fannin inda kididdiga daga kungiyar masana'antun samar da makamashi bisa hasken rana ta kasar Sin ta nuna cewa kamfanonin kasar Sin suna matsayi na daya a harkar samar da abubuwa masu mahimmanci guda hudu wadanda ake sarrafa makamashin hasken rana da su wato polycrystalline silicon, silicon wafers, da baturun cell, da sauran jiga-jigan sarrafawa. 

Kazalika, A cewar hukumar kula da makamashi ta kasar, ya zuwa karshen watan Yunin shekarar 2023, karfin makamashin da ake sabuntawa da aka girka a kasar Sin ya zarce kilowatt biliyan 1.3, wanda a karon farko ya zarce karfin da aka girka na makamashin kwal a tarihin kasar Sin. Karfin wutar lantarki kasar Sin bisa hasken rana da karfin iska, da ruwa, da nau’in makamashi daga wasu halittu yana kan gaba a duniya. 

Kamar dai yadda wakilin shugaban kasar Sin Xi Jinping na musamman Ding Xuexiang ya bayyana a yayin taron koli kan harkokin yanayi na duniya da ya gudana a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, ya kamata dukkan bangarorin su karfafa azama wajen tinkarar kalubalen sauyin yanayi tare. Yayin da take daukar kwararan matakai don yaki da dumamar yanayi, kasar Sin ta kuma bukaci kasashen duniya da su kiyaye manufofi da ka'idojin da aka gindaya a cikin yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD da yarjejeniyar Paris. (Muhammed Yahaya, Ibrahim Yaya, Sanusi Chen)