GCC ta yi kira da a dawo da tsagaita bude wuta a zirin Gaza
2023-12-06 10:49:58 CMG Hausa
An gudanar da taron koli na kungiyar hadin gwiwar kasashen yankin Gulf wato GCC karo na 44 a birnin Doha dake kasar Qatar jiya Talata, inda aka zartas da sanarwar Doha, inda ya bukaci a gaggauta maido da yarjejeniyar jin kai a zirin Gaza, domin cimma cikakkiyar yarjejeniyar tsagaita bude wuta mai dorewa, da kuma tabbatar da cewa, duk wani taimakon jin kai ya shiga yankin Zirin Gaza
Sanarwar ta jaddada cewa, ana fuskantar kalubale mai hadari a zirin Gaza, inda aka ta yi Allah wadai da tsananta rikici a zirin, a sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kaiwa zirin. Sanarwar ta yi kashedi cewa, idan kasar Isra’ila ba ta dakatar da kai hare-haren, da ci gaba da tada rikici ba, hakan na iya haddasa babbar illa ga tsaron jama’a dake wurin da ma zaman lafiya a duniya baki daya.
Sarki Tamim Bin Hamad Al Thani na kasar Qatar, ya bayyana a wannan rana cewa, dukkan bangarorin da suka halarci taron sun jaddada goyon bayansu ga Palesdinu da ta kafa kasarta mai cin gashin kanta.
Ofishin watsa labaru na kungiyar Hamas ta Palesdinu ya bayar da sanarwa a jiya cewa, tun bayan barkewar sabon rikici tsakanin Palasdinu da Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, mutane 16248 sun mutu a sakamakon hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai zirin Gaza, kana mutane fiye da dubu 43 sun ji rauni. (Zainab)