Yawan kunshin kayayyaki da aka isar a kasar Sin ya kai wani matsayi
2023-12-06 12:01:50 CMG Hausa
Masu kallonmu, barka da war haka. Hukumar kula da harkokin isar da sako ta kasar Sin ta fitar da bayanai a jiya Talata cewa, ya zuwa safiyar ranar 4 ga watan nan da muke ciki, yawan kunshin kayayyaki da aka isar a kasar Sin ya zarce guda biliyan 120, lamarin da ya nuna ci gaban karuwar harkokin sayayya a cikin kasa.