logo

HAUSA

An Bayyana Rawar Da Kasar Sin Ta Taka Kan Sauyin Yanayi Yayin Taron COP28

2023-12-05 14:06:35 CMG Hausa

Shugaban hukumar kula da makamashi ta duniya wato IEA Fatih Birol ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi fice a fannin gudanar da harkokin daidaita sauyin yanayi a duniya, tare da ba da gudummawa ga bangarorin kuduri da hikima, don tunkarar kalubalen da sauyin yanayi ke haifarwa.

Fatih Birol ya bayyana haka ne, a yayin taron kasashe masusa hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 28 wato COP28 dake gudana a birnin Dubai na hadaddiyar daular Larabawa. Yana mai cewa, ya kamata a fahimci cewa, an samu nasarori da dama a kasar Sin

Jami’in ya kuma bayyana a gyefen taron da aka gudanar a rumfar kasar Sin, yayin taron na COP 28 cewa, Sin ta samu gagarumin ci gaba a fannin samar da makamashi bisa karfin hasken rana da iska da motoci masu amfani da wutar lantarki da batura, haka kuma kasar Sin ta kasance ja gaba a duniya wajen samar da makamashi mai tsafta.(Ibrahim)