Bunkasuwar Sin na taka rawa ga farfadowar yankin Asiya da Pacific
2023-12-05 09:22:04 CMG HAUSA
DAGA MINA
IMF ta fitar da rahoton hange nesa kan bunkasuwar tattalin arzikin yankin Asiya da Pacific kwanan baya, inda ta yi hasashen cewa, yawan gudunmawar da bunkasuwar tattalin arzikin wannan yanki zai bayar a duniya a shekarar 2023 zai kai kashi 4.6%, wanda ya kai fiye da kashi 3.9% da aka yi hasashe a shekarar 2022, ban da wannan kuma, bankin raya Asiya ya ba da rahoto cewa, rawar da Sin take takawa kan bunkasuwar yankin ya kai 64.2%.
A matsayinsa na yankin da ya fi nuna kuzari a bangaren bunkasuwar tattalin arziki a duniya, yankin Asiya na cin gajiyar manufar bude kofa da hadin kan ciniki da zuba jari.
Sin na dukufa kan bude kofa da hadin kai da wasu kasashe dake yankin. A kwarya-kwaryan taron shugabannin APEC karo na 30, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sake jadadda wajibcin bude kofa, ya kuma ba da shawarar kiyaye ayyukan zuba jari cikin ’yanci bisa manufar bude kofa, da kuma nuna goyon baya da inganta tsare-tsaren ciniki karkashin jagorancin WTO, da kuma tabbatar da dorewar tsare-tsaren samar da kayayyaki a duniya, kazalika da adawa da siyasantar da batun ciniki da tattalin arziki, kuma bai kamata a rika alakanta batun ciniki da makamai da tsaro ba. Dole ne a nace ga ingiza samun bunkasuwar tattalin arzikin yanki na bai daya da gaggauta gudanar da ciniki cikin ’yanci.
Kokari da ci gaban da Sin take samu na zama karfi mai inganci ga farfadowar tattalin arzikin yankin. An yi imanin cewa, a cikin shekaru 30 masu zuwa, Sin za ta ci gaba da kara bude kofa da hada kai da sauran kasashen yankin, Sin za ta zama injin dake ingiza da tabbatar da bunkasuwa da wadata a yankin Asiya da Pacific. (Mai zana da rubuta: MINA)