logo

HAUSA

A kalla mutane 85 sun rasu sakamakon harin kuskure da sojojin Najeriya suka kaddamar a wani kauye

2023-12-05 20:53:39 CMG

Mahukunta a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya, sun tabbatar da rasuwar a kalla mutane 85, bayan da sojojin kasar suka kaddamar da harin bam ta sama, kan wani kauye dake karamar hukumar Igabi a jihar ta Kaduna.

Da yake tsokaci game da hakan cikin wata sanarwa, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Samuel Aruwan, ya ce tuni rundunar sojin kasar ta dauki alhakin kaddamar da harin na kuskure, yayin wani zama na masu ruwa da tsaki da ya gudana a jiya Litinin da jami’an gwamnatin jihar.

A Talatar nan kuma, shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya bayar da umarnin gudanar da bincike game da aukuwar lamarin. (Saminu Alhassan)