logo

HAUSA

Jami’in diflomasiyyar Falasdinu: PA ta godewa kasar Sin bisa aikewa da agaji ga ’yan Gaza cikin sa’o’in bukata

2023-12-05 10:14:42 CMG Hausa

Jakadar kasar Falsdinu a Masar ya mika godiyar kasarsa ga gwamnatin kasar Sin da jama’arta bisa yadda suka samar da kayayyakin jin kai a kan lokaci zuwa zirin Gaza da rikici ya dabaibaye.

Dial al Louh ya bayyana hakan ne a yayin wani bikin nuna godiya ga kasar Sin bisa taimakon da take bayarwa wanda ya gudana a ranar Lahadi a birnin Alkahira na kasar Masar, wanda ya samu halarcin jakadan kasar Sin a Masar Liao Liqiang da babban daraktan kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta Masar Rami Al-Nazer.

Ya kuma mika godiya da girmamawa na mahukuntar Falasdinawa da al'ummar Falasdinu ga kasar Sin bisa taimakon da take bayarwa a lokutan da al'ummar Gaza ke cikin bala'in jin kai.

A nasa bangaren, Al-Nazer ya ce, bangaren Masar ya yaba da yadda kasar Sin ke ba da agajin jin kai a zirin Gaza, kuma za ta ci gaba da ba da taimako wajen shigar da kayayyaki da rarraba kayayyakin. (Muhammed Yahaya)