logo

HAUSA

Ganawar musanya tsakanin kasashen Nijar da Rasha a birnin Yamai

2023-12-05 09:12:11 CMG Hausa

A jamhuriyar Nijar, tawagar kasar Rasha da ke ziyarar aiki ta yi zaman taro tare da bangaren kasar Nijar, inda a karshen ganawar bangarorin biyu sun cimma wasu yarjejeniyoyi a fannin soja da yaki da ta’addanci.

Daga birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, abokin aikinmu Mamane Ada na tare da ci gaban wannan labari.

Tawagar dake karkashin jagorancin mukadashin ministan tsaron Rasha janar kanal Lounous-Bek Evkourov na rangadin aiki tun ranar 3 zuwa 4 ga watan Disamban shekarar 2023 a Yamai, babban birnin kasar.

Inda a ranar ta jiya Litinin, wannan tawaga ta samu tattaunawa tare da takwarorinsu na kasar Nijar a karkashin jagorancin ministan tsaron kasar janar Salifou Modi. A tsakiyar wannan tattaunawa, karfafa dangantakar kasashen biyu a fannin tsaro da yaki da ta’addanci. Haka kuma, ganawar ta samu halartar manyan sojojin kasar Nijar da dama na matakai daban daban.

Jim kadan, bayan wannan zaman taro tsakanin manyan jami’an kasashen biyu, mista Evkourov da shi da jami’an dake rakiyarsa sun samu ganawa tare da shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP, kuma shugaban kasa, janar Abdourahamane Tiani a fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai.

A karshen wannan ganawa tare da shugaban kasar Nijar, mukadashin ministan tsaron kasar Rasha, ya jadadda goyon bayan kasarsa ga sabbin hukumomin Nijar a karkashin jagorancin CNSP bisa ga kokarin da suke na ganin kasar Nijar ta doshi hanyar ci gaba mai dorewa.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.