logo

HAUSA

Manyan Jami’an Najeriya Na Amincewa Da Alfanun Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ga Kasashen Afrika

2023-12-05 09:19:19 CMG HAUSA

DAGA MINA

 

A bana ake cika shekaru 10 da gabatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, kuma a farkon watan Oktoba, na ziyarci Najeriya, wadda take daya daga wasu kasashen Afrika wadanda suka riga sauran kasashen duniya amincewar shawarar. Domin fahimtar amfanin shawarar ga kasar, na zanta da kakakin majalisar wakilai, da ministan harkokin wajen kasar.

Kakakin majalisar wakilan Najeriya Abbas Tajudeen ya ce, “Tashar teku ta Lekki da kamfanin CHEC ya gina, da layukan dogo, da sauran ayyukan da kamfanin CCECC ya gudanar, da ma yankin ciniki maras shinge na Lekki, da na Ougun da Guangdong da sauransu, ba ma kawai sun samar da dimbin guraben aikin yi ba ne, har ma sun ingiza bunkasuwar tattalin arziki ga al’ummar wurin.” Shawarar na amfanar al’ummar Najeriya matuka, kuma kasarsa za ta ci gaba da goyon bayan shawarar, a cewar Abbas Tajudeen.

A nasa bangare kuwa, ministan harkokin wajen kasar Yusufu Tuggar cewa ya yi, “A matsayin kasa mai yawan jama’a kuma mafi karfin tattalin arziki a Afrika, shawarar ta dace da tsarin raya kasa. Kaza lika kasashen biyu suna hadin kai a fannin samar da manyan ababen more rayuwa, da horar da kwrarru, da dai sauran bangarori, ciki hadda tashar Lekki, da jirgin kasa dake Lagos, da layin dogon dake tsakanin Abuja da Kaduna, wanda ya kasance irinsa na farko a Afrika dake amfani da fasaha da ma’aunin Sin, da kuma sabon filin saukar jiragen sama na Abuja, wanda ya zama sabuwar alamar Abuja.

Ban da wannan kuma, na dawo nan kasar Sin a tsakiyar watan Oktoba,  inda na zanta da mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima, wanda ya halarci taron kolin kasa da kasa na tattaunawar hadin kai bisa shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na 3 a birnin Beijing, inda Shettima ya ce, shawarar na da babbar ma’ana ga bunkasuwar Afrika, wadda ta taka mihimmiyar rawa wajen samar da manyan ababen more rayuwa a kasashen. Alal misali a Najeriya, layukan dogo da kasashen biyu suka yi hadin kai wajen ginawa na da amfani matuka ga kafa tsarin zirga-zirga a kasar, da raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama’a. Layin dogon tsakanin Abuja da Kaduna da aka riga ake amfani da shi na ingiza bunkasuwar tattalin arziki da al’ummar Najeriya sosai. Ban da wannan kuma, Shettima ya ce, yayin zantawarsa da shugaban Sin Xi Jinping, sun kai ga matsaya daya, kan hadin kai a bangaren manyan ababen more rayuwa, kuma za a ci gaba da sa kaimi ga shimfida layukan dogo da dai sauran ayyuka a Najeriya.

Manyan jami’an Najeriya da dama suna amincewa da damammaki, da bunkasuwa da shawarar take kawowa kasashen Afirka, musamman ma Najeriya. A ganinsu, shawarar na taka rawa wajen raya manyan ababen more rayuwa, da kyautata zaman rayuwar jama’a, da daga karfin takarar kasarsu, har ma da samar da makoma mai haske a fannin hadin kai da cin moriya tare a nan gaba.

Ci gaban da Najeirya ke samu bayan ta shiga wannan shawara, ta zama misali ga amfanin shawarar ga Afrika har ma ga dukkanin fadin duniya. An yi imanin cewa, a cikin shekaru 10 masu zuwa, karin kasashe musamman ma kasashen Afrika, za su amince da wannan shawara da za su shiga, don more damammakin shawarar, da kuma kara amincewa tsakanin Sin da kasashen Afrika a bangaren siyasa, da al’adu, da hadin kan tattalin arziki, har ma ta kai ga taka rawa wajen samun zaman lafiya da karko a duniya baki daya. (Mai rubuta: Amina Xu)