logo

HAUSA

Libya ta tusa keyar 'yan ci-rani 147 zuwa Najeriya

2023-12-05 09:51:00 CMG Hausa

 

Hukumar kula da kaurar jama’a ta kasar Libya, ta sanar da dawo da bakin haure 147 da suka shiga kasar ba bisa ka’ida ba zuwa Najeriya.

Shugaban ofishin yada labarai da tantance muhimman takardun shigi da fici, Fathi Shnebbu ya ce, an tusa keyar wasu 'yan ci-rani 147 da suka shiga kasar ba bisa ka’ida ba daga Najeriya ta filin jirgin saman Tripoli Mitiga zuwa kasarsu. Ya ce, bakin hauren da aka kora sun hada da mata 122 da maza 25.

A cewar Shnebbu, wadancan bakin hauren sun shiga kungiyoyin masu aikata manyan laifuffuka, inda suka aikata laifukan da suka shafi safarar muggan kwayoyi, da safarar bindigogi, da kuma karuwanci.

Sakamakon rashin kwanciyar hankali da rudanin da ake fama da shi a kasar, tun bayan hambarar da gwamnatin marigayi Muammar Gaddafi a shekara ta 2011, 'yan ci-rani da dama wadanda galibi 'yan Afirka ne, suke kokarin tsallaka tekun Bahar Rum zuwa gabar tekun Turai daga kasar Libya.

A cewar hukumar kula da ‘yan ci-rani ta duniya, ya zuwa wannan shekara, an ceto jimillar bakin haure 15,057 ba bisa ka'ida ba, tare da mayar da su Libya.(Ibrahim)