logo

HAUSA

Manyan Jami’An Najeriya Sun Amince Da Ci Gaban Hadin Kai Karkashin Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”

2023-12-05 09:20:21 CMG HAUSA

DAGA MINA

Wasu kasashen yamma sun dade suna karawa ra’ayin tarkon bashin da Sin take baiwa Afrika gishiri, musamman ma bayan an gabatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, sun bayyana bashin da Sin take baiwa kasashen Afirka a matsayin abin da zai haifar da matsalar rikicin bashi.

Irin wannan kalamai na cewa wai bashin da Sin take baiwa Afrika tarko ne, da wasu kasashen yamma suka kirkiro, nufin sa shi ne hana bunkasuwar hadin kan Sin da Afirka da cin moriya tare.

Sinawa na da wani karin magana dake nuna cewa, idan ana son samun arziki, dole ne a gina hanyoyi da farko. Shi ya sa, rancen kudin da Sin take baiwa Najeriya don gabatar da ayyukan hadin kai karkashin wannan shawara, yawancin ayyukan ne na samar da manyan ababen more rayuwa. Alal misali, an gina layin dogo na farko mai amfani da ma’aunin Sin a Afrika, wato layin dogo dake tsakanin Abuja da Kaduna a Najeirya, da kuma layin dogo na farko dake cikin birni, wato layin dogo na Abuja na Najeirya.

A baya can tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari ya taba shaidawa manema labarai cewa, rancen kudin da Sin take baiwa Najeriya, an yi amfani da su ne wajen gina layin dogo, da hanyoyin mota da dai sauransu, kuma idan babu irin wadannan ayyuka, al’ummar kasar dai su yi zirga-ziraga da kafafu. Ya kuma yi maraba da duk wata kasa dake iya baiwa kasar taimako a fannin gina manyan ababen mora rayuwa.

Shin ko wadannan kasashen yamma ba su so sun shiga wannan aiki?

A farkon watan Oktoba na kai ziyara a Najeriya, na kuma zanta da kakakin majlisar wakilan kasar Abbas Tajudeen, kuma yayin zantawar mu ya ce, kasashe da dama suna shirin baiwa Najeriya rancen kudi, amma kasashen Afrika suna zabar irin da za su karbi rance bisa yanayin da suke ciki. Idan an kwatanta da manufofin sauran kasashe, rancen kudin da Sin take baiwa kasashe na kunshe da kudin ruwa mai araha, da wa’adi mai tsawo. Najeriya na godiya sosai kan taimakon da Sin take ba ta wajen raya tattalin arzikinta. Kuma bisa alkaluman da wasu hukumomin kasa da kasa, da kungiyoyin nazari suka bayar, an ce, yawancin basusukan da kasashen Afirka suke karba na fitowa ne daga daidaikun mutane na kasashen yamma.

Kasashen Afrika na da ma’uaninsu na zabar abokan hadin kai, bisa la’akari da moriyarsu. A halin yanzu, karin kasashe sun shiga shawarar “ziri daya da hanya daya”, kuma wasu manyan jami’an kasashen wadanda a da sun shiga gefen kasashen yamma, don karawa ra’ayin tarkon bashi gishiri, a yanzu suna shiga wannan shawara. Alkawarin da gwamnatin Sin ke yiwa kasashen dake shiga shawarar daddade ne, kuma dace da muradunsu, shi ya sa ta samu amincewa daga kasashe, da jama’arsu da suke shiga shawarar. Ban da wannan kuma, rancen kudin da Sin take baiwa kasashen, ana amfani da su ne wajen gina manyan ababen more rayuwa, matakin da zai ingiza bunkasuwar tattalin arzikinsu. Kaza lika idan an yi hangen nesa, za a ga cewa zai taimakawa wadannan kasashe wajen biyan bashin da kasashen yamma, da wasu hukumomin kudaden kasa da kasa suke binsu. (Mai zana da rubuta: MINA)