logo

HAUSA

Babban hafsan sojin Isra’ila: Sojojin Isra’ila sun kaddamar da farmaki a kudancin zirin Gaza

2023-12-04 11:26:14 CMG Hausa

Babban hafsan sojin Isra’ila Herzi Halevi ya bayyana a jiya Lahadi cewa, sojojin Isra’ila sun kaddamar da yaki a kudancin zirin Gaza a ranar 2 ga wata, yayin da za su ci gaba da tabbatar da nasarar da suka samu a arewacin zirin Gaza.

A cewar wata sanarwar da rundunar sojin kasar Isra’ila ta fitar a jiya Lahadi, Halevi ya ce sojojin Isra'ila sun kashe wasu kwamandojin kungiyar gwagwarmayar Islama ta Hamas a farmakin da suka kai a arewacin zirin Gaza a cikin kwanaki biyun da suka gabata, inda suka fara kai farmaki makamancin haka a kudancin zirin Gaza a safiyar ranar 2 ga wata. Kakakin rundunar sojin Isra'ila Daniel Hagari ya bayyana a wani taron manema labarai da yammacin jiya Lahadi cewa, sojojin na Isra'ila suna fadada hare-haren ta kasa zuwa "dukkan yankunan zirin Gaza." (Yahaya)