logo

HAUSA

Da Na Gaba Ake Gane Zurfin Ruwa

2023-12-04 19:13:43 CMG Hausa

A watan Satumba na shekarar 2020, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin na da burin kawar da sinadarin carbon dioxide kafin shekarar 2030, da kuma cimma matsaya game da kawar da iskar carbon gaba daya kafin shekarar 2060. A watan Nuwamban bana, a taron San Francisco, Sin da Amurka sun yanke shawarar yin hadin gwiwa a karkashin kungiyar aiki kan inganta yanayi. La’akari da ayyuka masu inganci wadanda ba a taba yin irinsu ba game da inganta yanayi, Sin ta zama babbar mai shiga tsakani, mai ba da gudummawa, kuma jagora a harkokin yanayi na duniya. Shi ya sa kasashen duniya suka sallama ma kasar Sin jagorancin magance sauyin yanayi saboda da na gaba ake gane zurfin ruwa.

Tarihi ya tabbatar da irin gwagwarmayar da kasar Sin ta yi kafin ta kai ga wannan matsayi na jagora a harkokin inganta yanayin duniya. A zamanin da, gidajen wanka na jama'a inda za ka biya kudi kadan sa’annan ka yi wanka da ruwan zafi sun kasance "ababen kallo" na musamman a biranen kasar Sin. Saboda ba a cikin sauki ake iya samun ruwan zafi na wanka a gidajen mutane ba.  

Amma a yau, wadannan gidajen wanka na jama'a wadanda ke fitar da iskar carbon mai dumama yanayi suna zama tarihi a hankali. Ci gaba a fannin fasahar samar da na’urar dafa ruwa mai amfani da hasken rana ta kawo sauki ga al’umma wajen samun biyan bukata ba tare da gurbata muhalli ba wanda ya daidaita kasar Sin a kan turbar rayuwa mai karancin iskar carbon.   

Daga kayan masarufi masu aiki da makamashin hasken rana zuwa samar da wutar lantarki, kasar Sin ta kasance jagora a cikin masana'antar samar da makamashi bisa hasken rana. Sama da shekaru goma da suka gabata, masana'antar makamashin hasken rana ta kasar Sin ta dogara kacokan ga kasashen waje wajen samar da albarkatun kasa da fasaha.  

A yau, kididdiga daga kungiyar masana'antun samar da makamashi bisa hasken rana ta kasar Sin ta nuna cewa kamfanonin kasar Sin suna matsayi na daya a harkar samar da abubuwa masu mahimmanci guda hudu   wadanda ake sarrafa makamashin hasken rana da su wato polycrystalline silicon, silicon wafers, da baturun cell, da sauran jiga-jigan sarrafawa.

Ci gaban da kasar Sin ta samu a masana'antar sarrafa wutar lantarki bisa hasken rana ya nuna aniyar kasar na aiwatar da manufofinta na fitar da karancin sinadarin carbon da kuma magance matsalar sauyin yanayi a duniya. Tun daga shekarar 2022, kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri a sabbin makamashi da suka hada da wutar lantarki mai aiki da hasken rana da kuma karfin iska, wanda ya haifar da raguwar dogaro da albarkatun waje na mai da iskar gas a cikin shekaru 30 da suka gabata.

A cewar hukumar kula da makamashi ta kasar, ya zuwa karshen watan Yunin shekarar 2023, karfin makamashin da ake sabuntawa da aka girka a kasar Sin ya zarce kilowatt biliyan 1.3, wanda a karon farko ya zarce karfin da aka girka na makamashin kwal a tarihin kasar Sin. Karfin wutar lantarkin kasar Sin bisa hasken rana da karfin iska, da ruwa, da nau’in makamashi daga wasu halittu yana kan gaba a duniya.

Kamar dai yadda wakilin shugaban kasar Sin Xi Jinping na musamman Ding Xuexiang ya bayyana a yayin taron koli kan harkokin yanayi na duniya da ya gudana a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, ya kamata dukkan bangarorin su karfafa azama wajen tinkarar kalubalen sauyin yanayi tare. Yayin da take daukar kwararan matakai don yaki da dumamar yanayi, kasar Sin ta kuma bukaci kasashen duniya da su kiyaye manufofi da ka'idojin da aka gindaya a cikin yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD da yarjejeniyar Paris, da inganta hadin kai da hadin gwiwa, da samun moriyar juna da samun nasara tare. A yayin da ake fuskantar rikice-rikice a duniya, hadin gwiwa ce kawai mafita. (Muhammed Yahaya)