logo

HAUSA

Yin Aiki Ba Tare Da Gajiyawa Ba A kan Kasa Mai Albarka

2023-12-04 14:35:52 CMG Hausa


Kafin ta yi ritaya, a watan Yulin shekarar 2023, Qin Guangwei ta kasance mataimakiyar shugaban kwalejin kimiyyar aikin gona ta Yancheng, wani birni na lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin. A matsayinta na mai fasahar noma, a cikin shekaru talatin da suka gabata, ta himmatu wajen bunkasa noman hatsi, da kuma kiyayewa da inganta kasa.

Yayin da ake yada dabarun noma a tsakanin manoma, mazauna karkara da yawa a birnin Yancheng sun amince sun karbe ta a matsayin amintacciyar abokiyar kud-da-kud. Ganin irin nasarorin da ta samu, ta samu lambobin yabo da dama a tsawon shekaru. Misali, ta sami lambar yabo ta ma’aikata mafiya nagarta na duk fadin kasar Sin, kuma an yi ma ta lakabi da suna ta mace mafi nagarta ta kasar Sin, da kuma babbar ma’aikaciyar kasar.

Qin Zhiyi, mahaifin Qin Guangwei, shi ma masanin aikin gona ne. A ‘yan shekarunta, Qin Guangwei tana jinjinawa yadda mahaifinta ya jajirce wajen yin sana'arsa, da kuma kaunarsa ga mazauna karkara da kasar noma mai albarka. Qin Guangwei, tun tana ‘yar karama ta kudurci    bin sawun Qin Zhiyi.

A shekarar 1987, ta fara aiki a ofishin kula da harkokin noma da karkara na Yancheng, jim kadan bayan ta kammala makarantar koyon aikin gona ta Yancheng, makarantar koyar da sana’o’i da aka jingina wa alhakin koyar da matasan karkara.

A cikin dan kankanin lokaci, an tura Qin Guangwei aiki a wani kauye da ke Yancheng. Da farko wasu daga cikin manoman sun yi ta tambayar ko ita, ‘yar birni wayeyya, za ta iya jurewa wahalhalun aiki da yanayin rayuwa a yankunan karkara. Ta tabbatar, ta hanyar ayyukanta, cewa tana da karfi da juriyar gudanar da aikin. 

Yayin da take aiki tukuru don habaka kwarewarta, ta yi koyo daga kwarewar mazauna karkara game da aikin noma. Sannu a hankali ta samu amincewar manoma da yawa, wadanda suka dauke ta kamar danginsu.

Qin Guangwei ta ce, "la’akari da kalaman mahaifina a cikin kai na, ko yaushe ina mu’amala da mutane da gaskiya. A sakamakon haka, mutane da yawa, ciki har da manoma, sun zama abokaina na kud-da-kud."

Zuciyarta tana cike da ni'ima a duk lokacin da manomi ya gaya mata cewa ya samu karin hatsi ko inganta amfanin gona da 'ya'yan itatuwa ta hanyar amfani da ilimin kimiyya da fasaha da Qin Guangwei ta koyar game da noma.

Qin ta ce, "A cikin 'yan shekarun nan, masana aikin gona da yawa sun inganta karfinsu na yada fasahohin aikin gona a tsakanin manoma. Duk da haka, ya kamata ma'aikatan su gudanar da bincike a yankunan karkara a fadin kasar, ta yadda za su kara fahimtar matsalolin manoma wajen noma."  

Ko da yake Yancheng na da mafi girman filin noma a Jiangsu, wasu filin noman daga cikin kasarta na dauke da gishiri mai yawa, wanda ke haifar da karancin amfanin gona. A cikin shekaru da dama da suka gabata, Qin Guangwei ta ci gaba da jajircewa kan burinta na asali, wato taimaka wa manoma su sami ingantacciyar rayuwa. Ta kuma jagoranci takwarorinta wajen yin amfani da dabarun noma na zamani don inganta yanayin kasa na Yancheng, ta yadda manoma za su kara yawan noman hatsi.

Ganin yadda suka jajirce wajen habakawa da amfani da dabarun noma don inganta kasa, kasar da a baya ba ta iya samar da hatsi da yawa saboda tana dauke da sinadarin saline-alkali mai dandanon gishiri ta sauya zuwa rumbun ajiyar hatsi. Sakamakon haka, Yancheng ya zama muhimmin tushen samar da hatsi a kasar.

Don taimakawa manoma su kara yawan amfanin gona, Qin Guangwei ta jaddada cewa ya kamata masu fasahar aikin gona su yi kokarin kara inganta kasa. Ta kuma jaddada cewa ya kamata masu fasaha su yi amfani da ilimin kimiyya da fasaha wajen noma, ta yadda za su taimaka wa manoma wajen inganta amfanin gonakinsu. Ta yi imanin cewa, hakan zai inganta habaka harkokin noma.

Qin Guangwei ta ce, "Kasa tana da rai, kamar dan Adam, za ta biya ku sakamakon kulawar da take samu. Duk da haka, idan ba ku taskace ta ko ba ku kare ta ba, ko ma kuka cutar da ita, kasa za ta kawo muku bala'i."  

Qin Guangwei har yanzu tana cikin damuwa game da halin rayuwar mazauna karkara, duk da cewa ta yi ritaya daga Kwalejin Kimiyyar Noma ta Yancheng. A ko da yaushe a shirye take don taimaka wa manoma su magance matsalolin fasaha a aikin su. "Zuciyata a cike take da ni'ima, yayin da nake aiki da manoma a gonaki," in ji Qin Guangwei.

A cikin shekarun da suka wuce, Qin Guangwei ta yi aikinta a matsayin mai fasahar aikin gona, kuma ta yi nazari kan hanyoyin bunkasa aikin gona. Qin Guangwei ta ce, "Burina na tsawon rayuwata shi ne in yi nazarin yadda zan samu yawan amfanin gona, da yadda ake kiyaye da inganta kasa."  (Kande Gao)