Nakasa ba kasawa ba ce
2023-12-04 12:11:04 CMG Hausa
Guo Jiaxun, mai shekaru 25 da haihuwa, wani mai hidimar aikewa da sakwanni ne a gundumar Deqing ta birnin Huzhou na lardin Zhejiang. Guo ya rasa kafarsa ta dama, sakamakon wani hatsarin mota, lokacin da yake da shekaru 6, amma bai yi kasa a gwiwa ba inda ci gaba da kokarin samun abun yi. Ya ce, nakasa ba kasawa ba ce, idan ya yi kokari, shi ma zai samu rayuwa mai kyau. (Murtala Zhang)