logo

HAUSA

Sojojin Somaliya sun kashe mayakan al-Shabab 60 a yankin tsakiyar kasar

2023-12-04 11:25:16 CMG Hausa

A safiyar Lahadi ne sojojin kasar Somaliya (SNA) suka kashe mayakan al-Shabab 60 tare da raunata wasu da dama a wani farmakin hadin gwiwa da suka kai kusa da garin Halgan da ke tsakiyar kasar Somaliya, a cewar gwamnatin kasar.

Sanarwar da ma’aikatar yada labarai, al’adu da yawon bude ido ta kasar ta fitar a Mogadishu, babban birnin kasar ta bayyana cewa, an kai harin ne kan ‘yan ta’addan al-Shabab da kwamandojinsu da ke hada gangami domin kai hari a yankunan tsakiyar kasar Somaliya.  

SNA da abokan hadin gwiwa na kasashen duniya sun kuma lalata sansanonin ‘yan ta’adda da makamai da dama a yankunan. Sojojin na ci gaba da bin sawun ‘yan ta’addan da suka tsere daga wurin, a cewar ma’aikatar.

Kungiyar ta al-Shabab dai ba ta ce komai ba game da sabon harin da sojojin suka kai. (Yahaya)