logo

HAUSA

Kila yadda a kan yi mummunan mafarki bayan shiga matsakaitan shekaru na rayuwa yana da nasaba da cutar karancin basira

2023-12-04 09:16:33 CMG Hausa

 

Masu karatu, ko ku kan yi mummunan mafarki kullum? Masu nazari na kasar Birtaniya sun gano cewa, bayan shiga matsakaitan shekaru na rayuwa, idan wasu su kan yi mummunan mafarki kullun, to, watakila barazanar da suke fuskanta wajen kamuwa da cutar karancin basira a nan gaba za ta karu.

Masu nazarin daga jami’ar Birmingham sun tantance bayanan da suka shafi mutane na rukunoni 2, wato wasu ‘yan shekaru 35 zuwa 64 a duniya dari 6 da 5, wadanda ba su da wata matsala a kwarewar fahimta, da kuma wasu tsoffi dubu 2 da dari 6 ‘yan shekaru 80 ko fiye da haka, wadanda ba su kamu da cutar karancin basira yayin da aka fara nazarin ba. An dauki shekaru 9 ana bibbiyar wadannan masu matsakaitan shekaru. A lokacin da aka fara nazarin da kuma lokacin da aka kammala nazarin, an jarraba kwarewarsu ta rike abubuwa, da gabatar da rahoton al’adarsu ta yin barci da yadda suka yi mummunan mafarki da dai sauransu.

Manufar jarraba kwarewar rike abubuwa ita ce, kimanta tsananin lalacewar kwakwalwa. Yadda aka tsufa, kan haifar da lalacewar kwakwalwa. Amma yadda lalacewar kwakwalwa ta yi sauri fiye da kima, watakila zai alamta kamuwa da cutar karancin basira.

An dauki shekaru 5 ana bibbiyar tsoffin a fannonin yin barci, da yin mummunan mafarki. Masu nazarin sun tabbatar da wadannan tsoffi sun kamu da cutar karancin basira ko a’a bisa bayanansu na ganin likita.

Sakamakon nazarin ya nuna cewa, a cikin ‘yan shekaru 35 zuwa 64 a duniya, in an kwantanta su da wadanda ba sa yin mummunan mafarki, wasu wadanda su kan yi mummunan mafarki a kalla sau 2 a ko wane mako sun fi samun karuwar hadarin lalacewar kwarewar fahimta har sau 4. A cikin tsoffin kuma, idan su kan yi mummunan mafarki kullum, to, yiwuwar kamuwa da cutar karancin basira ta fi yawa har sau 2.

Masu nazarin suna ganin cewa, yin mummunan mafarki, ba dalili ba ne na kamuwa da cutar karancin basira. Watakila lalacewar wani sashen kwakwalwa ce ta haddasa karancin basira.

Ya zuwa yanzu ba a iya shawo kan cutar karancin basira ba. Amma ana iya dakatar da tsanantar cutar ta hanyoyin cin abinci masu amfanar lafiya da kuma rika motsa jiki.

Masu nazarin sun bayyana fatansu na ganin sakamakon nazarinsu ya taimaka wajen gano barazanar kamuwa da cutar karancin basira tun da wuri, ta yadda za a dauki matakai masu dacewa. (Tasallah Yuan)